Posts

Showing posts from October, 2021

RANA (THE SUN)

Image
  SCIENCE IN HAUSA: GRAND EPISODE 14 KARSHEN BABI NA FARKO RANA (THE SUN) Yau da gobe mukan wayi gari da haske wanda muke samu daga halitta mafi girma a cikin taurari. Wannan babbar halitta tanada sunaye dayawa amma a Hausance muna kiranta da Rana. Wannan kashin na SCIENCE IN HAUSA gagarumi ne domin shine zai rufe Babin Farko na ayyukana. Rana ta samu ne kimanin shekaru biliyan 4.5 daga tarwatsewar gajimare mai dauke da burbushin Hydrogen. Masana kimiyya sunawa wannan al'amari lakabi da "Big Bang Theory" wanda akansa ne mafi yawan ilmin kimiyya na taurari ya ta'allaka. Rana tana daukene da shimfidu har guda shida wadanda suka hada da; 1- Corona: Itace shimfidar farko wacce take fitarda hasken rana izuwa sauran Duniyoyin da suke zagaye da Ranar. 2- Mafitar Kyalli (Chromosphere): Wannan shimfida itace take canza siffar mahaski (photon) izuwa haske kafin yakai ga Corona. 3- Mafitar Wuta (Photosphere): Kafin mahaski yakai ga fita waje yana sauya launi ne daga burbushin He