Posts

Showing posts from January, 2022

SARARIN SATURN (Planet Saturn)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: Babi Na 2 Kashi Na 5 SCIENCE IN HAUSA ๐Ÿ“š๐Ÿ’ก: SARARIN SATURN (Planet Saturn) Falakinmu cike yake da ababan al'ajabi, kama daga tarin bangorai masu yawo cikin sarari da kuma duniyoyi har guda takwas da suke zagaye rana. Daya daga cikin wadannan duniyoyin itace Saturn: ta biyu a mafi girma bayan Jupiter. Wannan kashin zamu tattauna ne akan sararin Saturn. Sararin Saturn itace ta biyu a mafi girma: da za'a ce a jera duniyar nan tamu a cikinta, sai an jera guda goma a mike kafin su kure tsawonta. Tanada launin ruwan zinare saboda irin sanadaran da suke cikinta kamar iskoki, narkakkun sinadarai da kuma sinadarin ammonia mai launin lu'u-lu'u. Wadannan iskokin sune na hydrogen da helium wadanda sune da mafi rinjaye na gaba daya nauyin sararin; kama daga gajimare har zuwa doron kasa. Hakanne yasa babu cikakkiyar turbaya a Saturn saboda tarin wadannan iskoki da suka sanya sararin batada nauyi. Zakuyi mamaki idan nace koda za'a samu teku mai fadin dazai iya d