Posts

Showing posts from December, 2023

Sauyin Yanayi (Climate Change)

Image
 Sauyin yanayi (Turanci: Climate Change) wani irin sauyi ne mai tasiri wanda ya shafi yanayin zafi, tsarukan damina, hunturu ko bazara a Duniya. WaÉ—annan sauye-sauye suna samuwa ne saboda irin ayyukan da mutane sukeyi gurÉ“atattu kamar Æ™one-Æ™onen abubuwa masu guba, da kuma sare dazuka ko bishiyoyi. WaÉ—annan abubuwan suna sanya sinadaran iskoki masu riÆ™e zafi su yawaita, ana masu laÆ™abi da greenhouse gases. Yawaitar waÉ—annan iskoki suna sanya yanayi ya sauya ta hanyoyi kamar haka: 1. Yawan zafin yana iya kawo fari ta yanda Æ™asa zata rasa danshi sakamakon rashin bishiyoyi. Hakan yana kawo Æ™arancin kayan gona sakamakon rashin samun wadataccen ruwan dazai taimaka wajen noma. 2. Dalili na sama yana kaiwa ga taÉ“a lafiyar mutane, musamman Æ™ananan yara. Rashin wadatar iskar numfashi ta oxygen daga bishiyoyin da aka sare na iya kaiwa ga taÉ“a lafiyar Æ™waÆ™walwa. 3. Yawaitar zafi kan iya É—umama Duniyar baki É—aya. Babban Æ™alubalen anan shine narkewar manyan dusar Æ™anÆ™ara wanda hakan yake kawo ambali