TSATSA (RUSTING)
SCIENCE IN HAUSA ๐๐ก: TSATSA (RUSTING) KASHI NA MUSAMMAN Abubuwa da dama sukan lalace tsawon lokaci bayan kirkirarsu; walau su rube, ko su dagargaje, ko su kece/yage ko kuma subi iska. Karafa sukan lalace ta hanyar yin wani abu mai suna tsatsa. A wannan karon zamu tattauna ne akan yanda karafa sukan lalace da dalilan yin hakan. Tsatsa (Turanci: Rusting) wani irin nau'ine na rubewa da yake shafar wadansu daga cikin karafa. Abinda yasa nace wasu shine; duk da tarin karafa da muka sani, ba kowanne bane yakeyin tsatsa. Wannan ya ta'allaka ne da dabi'un kwayoyin zarrar cikin kowanne karfe. (Duba kashi akan "Kwayar Zarra" domin karin bayani). Tsatsa tafi shafar bakin karfe wato Iron (Fe) saboda karfin sauyawarsa yayin daya hadu da wasu burbushin sinadarai. Wannan nau'in lalacewa na bakin karfe (Fe) yana faruwa ne yayin da kwayoyin zarrarsa suka hadu dana iskar oxygen (O2) da kuma ruwa (H2O): ana yiwa wannan hadaka lakabi da "redox reaction" wacce a Hau