DAMARAR ASTEROID (THE ASTEROID BELT)
SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 11 Sararin samaniya cike take da abubuwa da suke sanyawa ma'abota kwakkwafi zumudin ganewa idanunsu al'ajabin da yake tattare dasu. Damarar Asteroid (Turanci; Asteroid Belt) tana daya daga cikin tarin abubuwan mamakin dake kewaye da Duniyarmu. Wannan kashin na SCIENCE IN HAUSA zaiyi dubane ga bayanan da suke tattare da Damarar Asteroid. Damarar Asteroid wani yankine a sararin samaniya mai tattare da tarin duwatsu da bangorai da yake tsakanin duniyoyin Mars da kuma Jupiter; ana yiwa yankin da yake lakani da "Inner and Outer Planets Zone". Giuseppe Piazzi na kasar Italia shine wanda ake jinginawa gano Damarar Asteroid a cikin karni na Goma Sha Tara a shekarar 1801. Damarar Asteroid tana gewaya Rana ne kamar sauran duniyoyi sannan kuma yanada nisan a kalla kilomita tsakanin miliyan 327 zuwa 498 daga Ranar. A baya, masana kimiyya suna daukar duwatsu da kuma bangoran dake yankin Damarar Asteroid a matsayin wani yanki na wata Duniya data wanzu kaf