DAMARAR ASTEROID (THE ASTEROID BELT)


 SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 11

Sararin samaniya cike take da abubuwa da suke sanyawa ma'abota kwakkwafi zumudin ganewa idanunsu al'ajabin da yake tattare dasu. Damarar Asteroid (Turanci; Asteroid Belt) tana daya daga cikin tarin abubuwan mamakin dake kewaye da Duniyarmu. Wannan kashin na SCIENCE IN HAUSA zaiyi dubane ga bayanan da suke tattare da Damarar Asteroid.

Damarar Asteroid wani yankine a sararin samaniya mai tattare da tarin duwatsu da bangorai da yake tsakanin duniyoyin Mars da kuma Jupiter; ana yiwa yankin da yake lakani da "Inner and Outer Planets Zone". Giuseppe Piazzi na kasar Italia shine wanda ake jinginawa gano Damarar Asteroid a cikin karni na Goma Sha Tara a shekarar 1801. Damarar Asteroid tana gewaya Rana ne kamar sauran duniyoyi sannan kuma yanada nisan a kalla kilomita tsakanin miliyan 327 zuwa 498 daga Ranar.

A baya, masana kimiyya suna daukar duwatsu da kuma bangoran dake yankin Damarar Asteroid a matsayin wani yanki na wata Duniya data wanzu kafin ta tarwatse ko kuma suka rasa gurbin zama


. Wannan hasashen ba haka yake ba a yanzu duba da yanda ilmin kimiyya yazo da na'urori da suka sabawa hasashen a wajen bincike. Bincike ya nuna cewa Damarar Asteroid tana daukene da duwatsu da bangorai da bazasu gaza kasa da dubu metan ba; kuma a warwatse suke da tazarar mil 600,000 tsakanin juna. 

Damarar Asteroid tana daukene da wasu manyan bangorai har hudu wadanda sune suke dauke da mafi rinjaye na nauyin duwatsun. Wadannan bangorai sun hada da;

1- Vesta

2- Pallas

3- Hygiea

4- Ceres

Ceres shine bangorin da yafi kowanne nauyi a cikinsu. Yana dauke da rubu'in (1/4) nauyin Damarar Asteroid; nauyinsa yakai kashi 39. Damarar Asteroid tana dauke da wasu nau'ikan ma'adinai da ake fafutukar ganin an sarrafasu. Da za'a tattare dukkan duwatsu da bangoran Damarar Asteroid wuri guda, da bazasu fi ayi tafiyar kimanin kilomita 1500 akai ba. Sannan karfin jiwa (gravity) ta Jupiter ce take hana damarar kubcewa daga mazauninta (orbit).

A baya masana kimiyya suna daukar Damarar Asteroid a matsayin yankin mutuwa na na'urori saboda tunanin cunkoson duwatsu da bangoran wurin. Hakan ya gushe yayin da na'urar Pioneer 10 ta wuce ta cikin yankin a watan Yulin shekarar 1972. Masana suna kuma hasashen cewa dalilin bacewar karza/karzozi (dinosaurs) yana iya ta'allakane da Damarar Asteroid; ana hasashen cewa daya daga cikin duwatsun ne ya haddasa mutuwarsu miliyoyin shekaru a baya. 

Wannan yana daga cikin ingantaccen bayani gameda Damarar Asteroid. A gaba zanyi bayani akan Damarar Kuiper mai kamanceceniya da Damarar Asteroid. A cigaba da bibiyar SCIENCE IN HAUSA domin samun kayatattun bayanai a bangaren kimiyya da fasaha.

Na gode.

© Mubarak MS Jigirya

22/08/2021

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

ÆŠakika Guda Ta Falaki

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)