KWARKWATAR KIFI (Cymothoa exigua)

 SCIENCE IN HAUSA 📚💡





Daga cikin tarin halittun da basuda iyaka a wannan sararin na duniya, akwai masu amfani kamar kananun halittu masu taimakawa dan Adam narkar da sinadarai (enzymes); sannan kuma akwai masu zama a jikin sauran halittu (Parasite). Wadannan halittun sukan cutar ko kuma su taimakawa halittar da suke zama jikinta; daya daga cikinsu shine/itace Kwarkwatar Kifi.

Kwarkwatar Kifi (Turanci: Cymothoa exigua) wata karamar halitta ce da take zama a cikin teku, sannan kuma kwarin mannau ne (parasite) da suke zama a cikin kifaye. Wannan halitta tana daga cikin halittu masu kaurin fatar jiki (crustacean); launin Athropoda; sannan kuma zuri'ar Malacostraca. Wadannan halittu kuma kamar kwarkwata suke (louse) saboda dabi'ar ciyarwa ta hanyar tsotsan jini. Babban abun al'ajabi ga Kwarkwatar kifin shine: sunada dabi'ar sauya jinsi daga namiji zuwa mace saboda wanzuwar al'aurorin mace da namiji a tattare dasu. Ana masu lakabi da "Protoandritic Hermaphrodite"; wato mata-maza.

Wadannan halittu sukan shiga jikin kifine ta gefen kunnuwansa (gills) su zauna. Girmansu ya danganta; maza sukan kai tsawo tsakanin 7.5 mm zuwa 15mm; mata kuma tsawo tsakanin 8mm zuwa 29mm. Macen cikinsu tana danganawa da bakin kifin domin samawa kanta abinci saboda yin kwayaye. Yayin da ta isa bakin, saita sauka akan harshensa ta dinga tsotse jikin harshen: wannan ba karamar azaba bace saboda bayan lokaci jinin yana karewa. Yayin da ta samu nasarar zuke jinin harshen saiya kankance sannan ya tsinke ya fita daga bakin kifin.

Bayan nasarar fitar da harshen, macen Kwarkwatar takan soka kafafunta na baya a ramin harshen. Wannan zai bata damar zamowa sabon harshen kifin; ta yanda duk abincin da kifin ya hadiye saidai su raba tare. Idan kuma abincin bai samuba, takan zuke masa majinar jikinsa domin kore yunwa musamman idan tana dauke da ciki. Wannan cikin yana samuwa ne yayin da namijin kwarkwatar ya sadu da ita a cikin bakin kifin.

Yayin da aka kama kifin da yake dauke da wannan kwarkwatar, su kanyi kokarin fita daga bakinsa saboda gano alamun cewa mutuwa zaiyi. Mafi akasarin lokuta suna fitane ta inda suka shigo duk da cewa kofar ta kanyi kadan. Duk kifayen da suke ciki teku musamman wadanda mukeci irinsu shawa, sadin da sukumbiya; ko irinsu jan-baki, mahi-mahi da sauransu da ake samu a tekunan Pacifi ko Atlantic duk suna samun kutsen wadannan kwarkwatar yayin da suke kanana.

Saidai abun murna shine; wadannan kwarkwatar ba abinda sukeyi wa mutane. Amma saboda tsaro, za'a so a bude kifi domin kawar da kazanta.

Ma'anar Kalmomi:

*Crustacean - Halittun ruwa masu kaurin fata

*Protoandritic Hermaphrodite - Mata-mazan Kwarkwatar Kifi

*Mucus - Majinar Kifi

*Gills - Kunnuwan Kifi

*Louse/Lice - Kwarkwata

*Enzymes - Kananun Halittu Masu Kara Karfin Narkar Da Sinadarai

Na gode.

© Mubarak MS Jigirya

    27 February, 2022

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki