Posts

Showing posts from August, 2023

ZUCIYA (THE HEART)

Image
Zuciya tana ɗaya daga cikin tsoka mafi muhimmanci a jikin kowacce halitta; walau mutum ko dabba. Aikinta ya tattara ga samar da jini ga dukkanin sassan jiki ta hanyar wasu ɗakuna (chambers) guda huɗu, bututu da magudanai masu yawa. Waɗannan sune da alhakin samar da iskar numfashi (oxygen) tattare da sinadaran gina-jiki sun isa kowanne yanki a jiki. A yau, wannan kashin na KUNDIN SCIENCE IN HAUSA zai tattauna siffa da aikin kowane sashe na zuciya ne. Ɗakunan Zuciya Zuciya tana ɗauke da ɗakuna huɗu, waɗanda biyu suke a sama masu suna suna atrium ta dama da kuma atrium ta hagu. Sai kuma ɗakunan ƙasa guda biyu: ventricle ɗin dama, da kuma ventricle ɗin hagu. Atrium ta dama shine da alhakin karɓar jini wanda bai gauraya da iskar numfashi ba domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin dama da yake ƙasa. Atrium ta hagu kuma aikinta karɓar jinin daya gauraya da iskar numfashi domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin hagu. Amfanin ɗakunan ventricles shine fitar da jini daga cikin zuciya. Bututun Zuciya Zu