ZUCIYA (THE HEART)


Zuciya tana ɗaya daga cikin tsoka mafi muhimmanci a jikin kowacce halitta; walau mutum ko dabba. Aikinta ya tattara ga samar da jini ga dukkanin sassan jiki ta hanyar wasu ɗakuna (chambers) guda huɗu, bututu da magudanai masu yawa. Waɗannan sune da alhakin samar da iskar numfashi (oxygen) tattare da sinadaran gina-jiki sun isa kowanne yanki a jiki. A yau, wannan kashin na KUNDIN SCIENCE IN HAUSA zai tattauna siffa da aikin kowane sashe na zuciya ne.


Ɗakunan Zuciya


Zuciya tana ɗauke da ɗakuna huɗu, waɗanda biyu suke a sama masu suna suna atrium ta dama da kuma atrium ta hagu. Sai kuma ɗakunan ƙasa guda biyu: ventricle ɗin dama, da kuma ventricle ɗin hagu.


Atrium ta dama shine da alhakin karɓar jini wanda bai gauraya da iskar numfashi ba domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin dama da yake ƙasa. Atrium ta hagu kuma aikinta karɓar jinin daya gauraya da iskar numfashi domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin hagu. Amfanin ɗakunan ventricles shine fitar da jini daga cikin zuciya.


Bututun Zuciya


Zuciya tattare take da bututu masu yawa da suke gudanar da jini a ciki da wajenta, cikinsu akwai: babbar vena cava, ƙaramar vena cava, jijiyoyin pulmonary, sai kuma aorta.


Babbar vena cava da ƙaramar vena cava waɗansu jijiyoyi ne da suke ɗaukar jinin da bai gauraya da iskar numfashi ba daga sama da ƙasan gangar jiki izuwa atrium ta dama. Su kuma jijiyoyin pulmonary waɗansu magudanan jini ne guda huɗu masu ɗaukar jinin daya gauraya da iskar numfashi daga huhu izuwa atrium ta hagu.


Aorta kuma itace babbar jijiya a jiki mai gudanar da jinin daya gauraya da iskar numfashi daga ventricle ɗin hagu izuwa dukkanin sassan jiki.


Mahaɗar Zuciya


Zuciya tanada wani tsari mai ban sha'awa mai tattare da ƙwayoyin halittu masu tura saƙonnin masu fasalin lantarki domin samar da bugun zuciya bisa tsari. Wannan mahaɗar ta haɗa da:


1. Mahaɗar Sinoatrial: A cikin atrium ta dama take. Aikinta shine tura saƙonni masu assasa bugun zuciya.


2. Mahaɗar Atrioventricular: Ita kuma tana tsakanin atrium ta dama data hagune, da kuma tsakanin ventricle ɗin dama da hagu. Aikinta shine tsagaita bugun zuciya daki-daki ta hanyar matse ventricle ɗin.


3. Ɗaurin His: Waɗannan kuma ƙwayoyin halittu ne na musamman masu gudanar da saƙonnin lantarki a tsakanin mahaɗar Atrioventricular zuwa ɗakunan ventricle, ta hanyar matsesu da tatsar jini daga cikin zuciyar.


Tabbas, zuciya tsokace mai tattare da ababen al'ajabi ɗauke da ɓangarori mabambanta masu samar da iskar numfashi izuwa dukkanin sassan jiki.


Ma'anar Kalmomi


*Magudanar jini - Blood vessels

*Ƙwayoyin halittu - Cells

*Node - Mahaɗa

*Ɗakuna - Chambers

*Iskar Numfashi - Oxygen


Mubarak MS Jigirya

24 Agusta, 2023




Comments

Popular posts from this blog

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki