TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)

TSIBIRIN MACIZAI (ILHA DA QUEIMADA GRANDE)

A cikin tarin wuraren da suke da haɗari a doron duniyar nan, mutum bazai iya ƙidayo guda uku ba ba tareda daya lissafo da Tsibirin Macizai ba. Kafin mai karatu yace yau nazo da zance kamar tatsuniya, zanso a biyoni a hankali a kashin yau na Kundin Science In Hausa.

Tsibirin Macizai (Ilha Da Queimada Grande) wani yankine a kasar Brazil ta nahiyar Amurka ta Kudu wanda yake mai hatsarin gaske saboda halittun da suke cikinsa. Kimanin kilomita 33 daga birnin Sao Paulo shimfiɗe a cikin tekun Atlantic zaka tarar da wannan tsibirin mai ɗumbin mamaki. 

Tsibirin Macizai ya samo sunansa ne daga tarin macizan cikinsa wanda adadinsu yakai 4000. Macizan da sukayi kaka-gida a wannan tsibirin sune Zinariyar Kububuwa (Turanci: Golden Lancehead Viper) wadanda sukeda launuka daga kore da kuma na ruwan dorawa. Wadannan macizai sunada matukar ƙarfin dafi sau biyar fiyeda sauran kububuwar da suke kan tudu. A hasashe na tarihi ance wai 'yan fashin teku (Pirates) sune suka ajiyesu saboda tsaron dukiyoyinsu. A wani ƙaulin kuma akace wai masu gadin hasumiyar tsibirin ne suka kawosu. 

Baƙin tsuntsaye masu ziyartar wannan tsibirin sune suke zamowa abincin wadannan macizan. Abinda yasa nace "baƙi" shine; asalin tsuntsayen da suke rayuwa cikin tsibirin sun san duk wata dabara ta macizan wajen farauta: hakan yasa basu kamuwa cikin sauki. Yawan wadannan macizan yasa ba'a iya taku kafa uku zuwa hudu ba tareda an tarar dasu ba; walau a cunkuso ko a warware. Suna wanzuwa a saman bishiya ta hanyar basaja da ganyaye, ko kuma a cikin duwatsu da ramuka. Wannan yasa ba'a shiga tsibirin ba tareda kaya wadanda zasu kare mutum da cizonsu ba.

Tsibirin Macizai yana ƙarƙashin ƙasar Brazil ne; wanda dalilin hakan yasa ƙasar takeda ikon hana mutane zuwa tsibirin. Wadanda aka yarda su ziyarci wannan tsibirin sune masu bincike daga bangaren kimiyya kadai. Wannan yanada nasaba ne da hatsarin wurin da halittun cikinsa; aƙalla dafin Zinariyar Kububuwa guda zai iya kashe mutane manya har guda hudu ko biyar. Duk da haka, macizan suna bayar da gudunmawa wajen samar da magunguna na hawan jini da sauransu daga dafinsu.

Zanyi amfani da wannan damar wajen taya makaranta ayyukana murnar sabuwar shekarar Miladiyya ta 2023. Na gode matuka da irin goyon bayanku gareni.

📸: The What If Show

© Mubarak MS Jigirya
4 Janairu, 2023 

Comments

  1. Wannan ai abin tsoro ne

    ReplyDelete
    Replies
    1. Gaskiya kam. Amma ai Gwamnatin ƙasar bata bari a shiga saida izini.

      Delete
  2. Masha Allah, Allah ya kara basira

    ReplyDelete
    Replies
    1. Amin thumma Amin. Nagode 🙏

      Delete

Post a Comment

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki