KAREN RUWA (TARDIGRADE)
SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU KASHI NA BIYU (Episode 2) A cikin tarin halittu da suke wanzuwa cikin wannan duniyar tamu, mukan kasasu izuwa sashe daban-daban ta fuskar dabi'u, siffa ko yanayin cima. Mukan dauki zaki a mafi kwarjini, giwa mafi karfi, dila mafi wayo da sauransu... Dakata! Amma duk hakan ba abun mamaki bane idan kasan halittar TARDIGRADE; halitta mai dumbin al'ajabi da bayananta zasu zo kamar tatsuniya. Karen Ruwa (Turanci: Tardigrade) mai sunan kimiyya "Echiniscus succineus" wani irin launin halitta ne mai kankanta fiye da sauro da kafafu har takwas. Karen ruwa yanada tsawo kimanin milimita guda (1 millimeter) da kuma nauyi wanda bashida muhimmanci sosai. Yana daga cikin dangin halittu da akewa lakabi da "microorganisms"; ma'ana wadanda idanu basa iya gani saboda kankanta. A kiyasi na binciken malaman kimiyya, akwai akalla dangin karen ruwa kimanin 1100 da aka sani. Daga cikin abubuwa mafi mamaki gameda wannan halitta shine yanda take iy