JIMA (Tanning)
SCIENCE IN HAUSA: Episode 8 Jima (Turanci: Tanning Chemistry) wani nau'ine na kimiyya da yake samar da kirgi daga fatun dabbobin da muke yankawa domin ci da hadiya; kamar a Sallah Babba data gabata. Wannan kashin zai bamu damar ninkaya cikin ilmin sarrafa fatun dabbobi domin samar da kirgin da ake mana takalma, angara, kujeru da kuma suturu da sauransu. Yayin da aka kwabe fata daga jikin dabba anso a zuba mata wani yanki na gishiri domin tsayar da barnar kwayoyin halittun bakteriya masu sanyata wari da lalacewa. Wannan gishirin yana dauke danshin jikin fatar saboda kasantuwar gishiri sinadari mai tsotse danshi. Bayan hakan anso a bazata saboda samun wadatacciyar iska; ana iya fara sarrafata a take idan ba'a da niyyar ajiyeta na tsawon lokaci. Abu na farko a Majema (Turanci: Tannery) shine ware wadannan fatu a mazaunan kanana ko manya, cikakku da jemammu a matakin geometry; wannan akewa lakabi da "grading and selection" a harshen Turanci. Bayan anyi hakan