Duniyar Mars (Planet Mars)

 SCIENCE IN HAUSA: Episode 3

Duniyar Mars (Planet Mars)


A ilmin taurari, masana sun sanar damu gameda duniyoyi 9 da suke zagaye da rana wacce itace babbar tauraruwar da duniyoyin suke zagawa. Cikin wannan kashin na wannan satin zanyi bayani akan daya daga cikinsu, wato  Duniyar Mars wacce a turance akewa lakabi da Red Planet.


Duniyar Mars ta samune kimanin shekaru biliyan 4.5 a kiyasin Malaman kimiyya. Itace duniya ta 4 daga Rana bayan Mercury, Venus da Earth (duniyarmu), sannan itace ta biyu a mafi kankanta. Mars duniya ce mai kaurin tafiyar mil 4,212 daidai da kilomita 6,778 a ma'aunin diameter. Tanada farfajiya wacce take daidai da fadin nahiyoyin Duniyar Earth mai dauke da tarin duwatsu.


Red Planet da akewa Mars lakabi ya samo asaline daga tarin sinadarin iron da duniyar take dauke dashi. Wannan sindarin yana gauraya da iskar oxygen ya samar da tsatsa bisa turbayar duniyar; shine dalilan dayasa take da launin ja. Kwanson duniyar Mars tattare yake da sinadaran iron, nickel da sulphur wadanda suke lullube da ma'adanai na sinadarin silicate (turbaya) da kuma tsandauri cike da iron.


Duniyar Mars tattare take da sanyi mai tsanani wanda yakai -225 a ma'aunin Fahrenheit daidai da -142 a ma'aunin Celcius. Wannan dalilin ya sanya wanzuwar kwayoyin halittu ya zamto da wahala. Kogin Nili Fossae wani idon ruwane daya kafe kimanin shekaru biliyan 3.5 kuma shine yake nuni da wanzuwar ruwa akan Mars a wadannan shekarun da suka gabata. Ruwan dake kan Duniyar Mars yana daskare ne a matsayin kankara a wasu yankuna na Mars; ana kiransu solar ice caps.


Iskar dake gajimaren Mars tattare take da hadakar iskokin Carbon Dioxide, Argon, Nitrogen da kuma wani burbushi na Oxygen; a takaice gajimaren bashida kauri saboda hadakar iskokin. Abun al'ajabi shine yanda Mars take dauke da dutse mai aman wuta mafi girma a cikin duniyoyin dake zagaye Ranarmu; Olympus Mons ake kiransa. Kuma wannan dutsen ya ninka Mount Everest da tsawo sau 3. Tsakanin Duniyarmu da Mars akwai tazarar kilomita miliyan 261.54.


Duniyar Mars ta fara samun ziyartar sakwagwai daga Duniyar Earth ne a shekarar 1960 da jirgin Marsnik, sai Marsfoll, Nozomi II, Mars Express, Phoenix Lander da Insight sune suka biyo bayansa. Sakagon NASA mai suna Curiosity Rover shine da alhakin daukar hotuna da kuma samar da bayanai akan bincike. 


© Mubarak MS Jigirya

      04/07/2021

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

ÆŠakika Guda Ta Falaki

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)