CUTAR DAJIN FARJI (Vaginal Cancer)
KUNDIN SCIENCE IN: Tsokaci Maudu'i: Cutar Dajin Farji (Vaginal Cancer) Kwanakin baya nayi bayani akan cutar dajin ƙashi (leukaemia); haɗe da jawabin yanda take samuwa da maganinta. Kafin wannan nayi kuma akan cutar dajin mama (breast cancer). Cikin 'yan kwanakin nan nayita samun tambayoyi gameda cutar dajin farji, musamman daga ɗaliban ilmi. To a gurguje inason nayi bayani akan ita cutar dajin farji. Kamar yanda nayi jawabi a lakcocin baya: cutar daji tana samuwa ne daga gurɓatattun ƙwayoyin halittun da basu mutu ba a cikin jikin ɗan Adam. Waɗannan gurɓatattun ƙwayoyin halittun suna iya kama kowanne ɓangare a jikin mutum idan suka fara yawaita. Cutar dajin farji tana kama matane a cikin farjinsu ta hanyar farawa da samar da gyambo (tumour) kafin ta nuna kanta. Akwai waɗansu abubuwa daya kamata mace ta lura dasu; idan tana ganin yawaita afkuwarsu, ta tuntuɓi likita: 1- Fitsari haɗe da jini. 2- Fitar ruwa daga gabanta. 3- Yawaitar sauyin ɗanɗano a baki. 4- Kumburin m