CUTAR DAJIN FARJI (Vaginal Cancer)

KUNDIN SCIENCE IN: Tsokaci
Maudu'i: Cutar Dajin Farji (Vaginal Cancer)

Kwanakin baya nayi bayani akan cutar dajin ƙashi (leukaemia); haɗe da jawabin yanda take samuwa da maganinta. Kafin wannan nayi kuma akan cutar dajin mama (breast cancer).

Cikin 'yan kwanakin nan nayita samun tambayoyi gameda cutar dajin farji, musamman daga É—aliban ilmi. To a gurguje inason nayi bayani akan ita cutar dajin farji. 

Kamar yanda nayi jawabi a lakcocin baya: cutar daji tana samuwa ne daga gurɓatattun ƙwayoyin halittun da basu mutu ba a cikin jikin ɗan Adam. Waɗannan gurɓatattun ƙwayoyin halittun suna iya kama kowanne ɓangare a jikin mutum idan suka fara yawaita.

Cutar dajin farji tana kama matane a cikin farjinsu ta hanyar farawa da samar da gyambo (tumour) kafin ta nuna kanta. Akwai waɗansu abubuwa daya kamata mace ta lura dasu; idan tana ganin yawaita afkuwarsu, ta tuntuɓi likita:

1- Fitsari haÉ—e da jini.
2- Fitar ruwa daga gabanta.
3- Yawaitar sauyin É—anÉ—ano a baki.
4- Kumburin mara.
5- Fitar jini ba lokacin al'ada ba.
6- Rikicewar jinin al'ada akai-akai: tsawaitawa, gajarcewa ko raguwar kwanaki ba ƙakƙautawa.
7- Bayan gida haÉ—e da jini.
8- Ƙarancin jini.

A lura: Masana sunyi ittifakin cewa zuri'ar da ake samun yawaitar masu cutar daji tana cikin hatsari. Dalili kuwa shine saboda waɗannan ƙwayoyin halittun ana iya samunsu jikin 'ya'yansu.

Idan mace tana yawan fuskantar wasu daga cikin abubuwan dana lissafo a sama, ga abubuwan daya kamata tayi:

- Duba lafiyar jiki aƙalla sau ɗaya a shekara.
- Duba lafiyar jini da adadin sukari.
- Duba ƙwayayen haihuwa bayan shekaru biyu.
- Duba lafiyar mahaifa.

Sai kuma a kiyaye abincin da akeci tareda motsa jiki. Sannan a guji amfani da kayan mata masu É—auke da sinadarai masu iya cutarwa.

Allah Ya bamu lafiya; Amin.

-Mubarak MS Jigirya

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

ÆŠakika Guda Ta Falaki

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)