Posts

Showing posts from May, 2023

CIWON DAJI (Cancer)

Image
CIWON DAJI (CANCER) Ciwon daji (Turanci: Cancer) wani launin ciwone wanda yake samuwa sakamakon waɗansu dalilai da ilmin Kimiyya yake ta ƙoƙarin zaƙulo su kullum. Cutar daji tana daga cikin manyan cututtuka da Duniya take fama dasu a yanzu saboda sarƙaƙiyar dake tattare da magance cutar. A kiyasi, ɗaya cikin bakwai na kowacce mutuwa a Duniya ana samun mai cutar daji a ciki; misali kamar cutar daji ta huhu, nono, hanji da kuma sauransu. Jikin ɗan Adam tattare yake da ƙwayoyin halittu kimanin biyalin sau dubu wadanda idan suka samu matsala suke komawa gyambon cutar daji. Wadannan ƙwayoyin halittu sun haɗa da; 1- Epithelial: Waɗannan ƙwayoyin halittu sune suke kawo cutar daji a fatar mutum da kashi 80 zuwa 90. 2- Magamar Matattara (Connective Tissue): Wannan cutar ta daji itace wacce take shafar kayan ciki kamar 'yayan hanji, baki da mara. 3- Jini Da Ɓargo (Blood & Lymphatic): Wannan tana daga cikin mafi munin cutukan daji. Ƙwayoyin halittu na jini wadanda suka samu ma