CIWON DAJI (Cancer)

CIWON DAJI (CANCER)

Ciwon daji (Turanci: Cancer) wani launin ciwone wanda yake samuwa sakamakon waɗansu dalilai da ilmin Kimiyya yake ta ƙoƙarin zaƙulo su kullum. Cutar daji tana daga cikin manyan cututtuka da Duniya take fama dasu a yanzu saboda sarƙaƙiyar dake tattare da magance cutar. A kiyasi, ɗaya cikin bakwai na kowacce mutuwa a Duniya ana samun mai cutar daji a ciki; misali kamar cutar daji ta huhu, nono, hanji da kuma sauransu.

Jikin ɗan Adam tattare yake da ƙwayoyin halittu kimanin biyalin sau dubu wadanda idan suka samu matsala suke komawa gyambon cutar daji. Wadannan ƙwayoyin halittu sun haɗa da;

1- Epithelial: Waɗannan ƙwayoyin halittu sune suke kawo cutar daji a fatar mutum da kashi 80 zuwa 90.

2- Magamar Matattara (Connective Tissue): Wannan cutar ta daji itace wacce take shafar kayan ciki kamar 'yayan hanji, baki da mara.

3- Jini Da Ɓargo (Blood & Lymphatic): Wannan tana daga cikin mafi munin cutukan daji. Ƙwayoyin halittu na jini wadanda suka samu matsala sukan juye su koma cutar daji ta jini da ɓargo cikin kashi.

Yayin da waɗannan ƙwayoyin halittu suka samu tangarɗa wajen sauyin halitta, sukan rikiɗe izuwa gyambo mai girma da ake kira "tumor" a sassa daban-daban a jikin ɗan Adam. Wannan gyambon shine yake zama cutar daji bayan wani lokaci.

A ƙiyasi na Malaman kimiyya, suna danganta cutar daji da sauyin da ake samu a jikin wadansu masarrafun halitta a jikin ɗan Adam. Waɗannan masarrafun na halittu sun kasu izuwa kashi uku;

1- Proto-oncogene: Masu assasa girma da rabuwar ƙwayoyin halittu.

2- Tumor Suppressor: Sune da alhakin dakatar da rabuwar ƙwayoyin halittu.

3- DNA Repair: Wannan masarrafar itace da alhakin tsare bayanan halitta. 

Sauyi cikin waɗannan abubuwan dana lissafa sukan haifar da tsiron cutar daji wanda yake bazuwa izuwa sassan jiki ta hanyoyin jini. Gyambon ya kasu zuwa gida biyu, kamar;

1- Benign: Mai tattaruwa wuri guda. Wannan irin gyambo baya bazuwa a jikin dan Adam saidai ya tsaya wuri guda yayita girma tsawon lokaci.

2- Malignant: Mai bazuwa izuwa sassan jiki na dan Adam kenan. Wannan irin gyambo shine yake toho a wurare daban-daban tsawon lokaci kamar zare saboda karfinsa.

Dalilai da dama da suke kawo cutar daji sun hada da karfaffan zafi (radiation) daga rana, ciye ciye na abinci mai dauke da sinadarai masu guba, hayakin sigari da sauransu. Mafi munin cutar daji itace ta huhu (lungs cancer) mai kashe mutane aƙalla 154,050, sai ta hanji (colon cancer) da 50,630, ta kayan ciki (pancreatic cancer) da 44,330 sannan ta nono (breast cancer) da 41,400.

Ilmin kimiyya yanata daɗa faɗaɗa maganin cutar daji ta hanyoyin bincike domin daƙile gyambon kafin yakai ga zama ciwon. Waɗannan hanyoyi sun hada da amfani da haske (laser), ƙwayoyin (chemotherapy) da wasu magunguna daga tsirrai.

Cutar daji ta haɗa da ta kwakwalwa, baki, huhu, hanji, fata, maƙogoro, mara da sauransu. Muna fatan Allah Ya baiwa marasa lafiyar cikinmu sauki.

Wannan kashin tsokacine domin ya zamo manuniya da kuma karin ilmin akan cutar daji. Na gode.

-Mubarak MS Jigirya
7 Mayu, 2023

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

Ɗakika Guda Ta Falaki