ÆŠakika Guda Ta Falaki
KUNDIN SCIENCE IN HAUSA Ɗaƙiƙa Guda Ta Falaki Falaki (Turanci: Universe) cike yake da ababan al'ajabi, kama daga yawan duniyoyi (planets) da suke a warwatse, ɓangorai (asteroid ko comets), ɗamaru (Asteroid, Kuiper da Heliosphere), watanni na duniyoyi da kuma tarin taurari. Wannan Falakin namu kuma ɗayane daga cikin biliyoyin Falakan da suke waje. Idan ban manta na taɓa faɗa mana sunan namu Falakin, wato "Milky Way" a Turance. Wannan Falaki namu ya tara duniyoyi guda takwas, tareda sauran ƙananun duniyoyi da akewa laƙabi da "Dwarf Planets"; irinsu Pluto da makamantansu. To amma meye yake faruwa a kowacce daƙiƙa a cikin wannan Falaki? Masana kimiyyar ilmin falaki wato "Cosmologists" sunyi ittifaƙin cewa a kowacce daƙiƙa guda waɗansu abubuwa masu tarin al'ajabi suna faruwa a cikinsa, kamar: 1. Ana haihuwar taurari kimanin 3,180 a kowacce daƙiƙa. 2. Daga cikin taurarin da suke wanzuwa tsawon biliyoyin shekaru, guda 900 suna fashewa yayinda