Posts

Showing posts from February, 2022

KWARKWATAR KIFI (Cymothoa exigua)

Image
 SCIENCE IN HAUSA ๐Ÿ“š๐Ÿ’ก Daga cikin tarin halittun da basuda iyaka a wannan sararin na duniya, akwai masu amfani kamar kananun halittu masu taimakawa dan Adam narkar da sinadarai (enzymes); sannan kuma akwai masu zama a jikin sauran halittu (Parasite). Wadannan halittun sukan cutar ko kuma su taimakawa halittar da suke zama jikinta; daya daga cikinsu shine/itace Kwarkwatar Kifi. Kwarkwatar Kifi (Turanci: Cymothoa exigua) wata karamar halitta ce da take zama a cikin teku, sannan kuma kwarin mannau ne (parasite) da suke zama a cikin kifaye. Wannan halitta tana daga cikin halittu masu kaurin fatar jiki (crustacean); launin Athropoda; sannan kuma zuri'ar Malacostraca. Wadannan halittu kuma kamar kwarkwata suke (louse) saboda dabi'ar ciyarwa ta hanyar tsotsan jini. Babban abun al'ajabi ga Kwarkwatar kifin shine: sunada dabi'ar sauya jinsi daga namiji zuwa mace saboda wanzuwar al'aurorin mace da namiji a tattare dasu. Ana masu lakabi da "Protoandritic Hermaphrodite&quo