Posts

Showing posts from January, 2023

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)

Image
TSIBIRIN MACIZAI (ILHA DA QUEIMADA GRANDE) A cikin tarin wuraren da suke da haÉ—ari a doron duniyar nan, mutum bazai iya Æ™idayo guda uku ba ba tareda daya lissafo da Tsibirin Macizai ba. Kafin mai karatu yace yau nazo da zance kamar tatsuniya, zanso a biyoni a hankali a kashin yau na Kundin Science In Hausa. Tsibirin Macizai (Ilha Da Queimada Grande) wani yankine a kasar Brazil ta nahiyar Amurka ta Kudu wanda yake mai hatsarin gaske saboda halittun da suke cikinsa. Kimanin kilomita 33 daga birnin Sao Paulo shimfiÉ—e a cikin tekun Atlantic zaka tarar da wannan tsibirin mai É—umbin mamaki.  Tsibirin Macizai ya samo sunansa ne daga tarin macizan cikinsa wanda adadinsu yakai 4000. Macizan da sukayi kaka-gida a wannan tsibirin sune Zinariyar Kububuwa (Turanci: Golden Lancehead Viper) wadanda sukeda launuka daga kore da kuma na ruwan dorawa. Wadannan macizai sunada matukar Æ™arfin dafi sau biyar fiyeda sauran kububuwar da suke kan tudu. A hasashe na tarihi ance wai 'yan fashin te