KWAYAR HALITTA (THE CELL)
SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 13 Kowacce halitta walau mutum, dabba ko tsirrai suna tattare ne da wasu kananun ginshikai wadanda sune tushen gabobi da kuma tsokar jikinsu. Wadannan abubuwa sune kwayar halittu (Turanci: Cell or Cells) wadanda sune ginshikan kowacce siffar kowacce halitta. Sunada kankatar da ido baya iya ganinsu face da na'urar hangen nesa (microscope). Kwayar halitta/halittu (daga yanzu KH) sune mafi kankantar siffa a jikin kowacce rai. A jikin mutum kadai akan samu KH kimanin trillion 50; a jikin yatsa ana iya samun kimanin miliyan 10. Yayinda a jikin silin gashi guda ana iya jera KH guda 10 saboda kankantarsu. Misalin KH da akan iya gani da ido itace kwaiduwa (egg yolk) wanda KH ce guda mai zaman kanta. Amfanin KH sun hada da samar da kuzari da kuma sinadaran gina jiki. KH ta kashi izuwa kashi biyu; 1- Eukaryotic: Wadannan ana samunsu ne a jikunan mutane da tsirrai. KH din eukaryotic suna tattare da kayan ciki (Organelles) wadanda suke kunshe da wadansu abubuwa daya