Posts

Bikin Baje Kolin HIBAF 2025

Image
  Bikin Baje Koli Da Fasahohin Hausawa wani taro ne da yake gudana a kowacce shekara a ƙarƙashin Gidauniyar Open Arts. Bikin wanda ake yiwa laƙabi da HIBAF (Hausa International Book and Arts Festival) yana bayyana al'adun Hausawa ne ta hanyoyi mabambanta da suka haɗa da adabi, waƙoƙin baka da na zube, tattaunawa ta ga-mu-ga-ku, wasannin kwaikwayo, da sauransu. Taken bikin na wannan shekarar shi ne "Rumbunan Ilimi," wanda zai yi duba izuwa ga tushe da tsarin ilimin Hausawa tun kafin zuwan Musulunci, Larabawa da kuma Turawan Mulkin-mallaka. Bikin na wannan shekarar zai karkata ne ga tarin fasahohin Hausawa a fannonin rayuwa a da da kuma yanzu ta hanyar gayyato masana, gwaje-gwaje, da sauransu. Bikin HIBAF ba wai ga Arewacin Najeriya ya tsaya ba kaɗai, a'a; taro ne da yake samun halartar mutane daga sassa na Duniya. Kama daga Hausawa, da kuma masu sha'awar nazarin harshen Hausa da al'adun su. A yayin bitar bikin wanda ya gudana a harabar Open Arts ƙarƙashin jagor...

AMFANIN SUKARIN GLUCOSE

Image
  AMFANIN SUKARIN GLUCOSE Glucose nau'in sukari ne da ake yiwa laƙabi da "monosaccharide," wato dangin sukari mai rukuni ƙwayar zarra (molecule) ɗaya. Daga cikin wannan dangi akwai irinsu galactose da fructose, waɗanda sune suke haɗuwa su samar da cikakken sukari mai rukunin ƙwayar zarra biyu, wato "disaccharide." Dukannin wani nau'in sukari yana samuwa ne daga dangin abinci na carbohydrates, wato launukan abinci masu samar da kuzari da gina jiki irinsu shinkafa, dankali, gwaza, masara, da sauransu. Su kuwa waɗannan dangin abinci ɗauke suke da sinadaran hydrogen, carbon, da oxygen. Amfanin glucose a jiki ya haɗa da: 1. Samar da kuzari ga dukkanin ƙwayoyin halitta a jiki, wato cells. 2. Taimakawa ƙwaƙwalwa wajen gudanar da aiki cikin sauƙi. 3. Yaƙar cutukan ƙwaƙwalwa kamar Alzheimer da Parkinson. 4. Samar da lafiyar fata ta fuskar wadatar danshi da kore tamoji. 5. Ƙarawa ƙasusuwan jiki ƙwari, da kuma taimaka masu wajen gudanar aikin ƙarfi. 6. Glucose na taima...

Sauyin Yanayi (Climate Change)

Image
 Sauyin yanayi (Turanci: Climate Change) wani irin sauyi ne mai tasiri wanda ya shafi yanayin zafi, tsarukan damina, hunturu ko bazara a Duniya. Waɗannan sauye-sauye suna samuwa ne saboda irin ayyukan da mutane sukeyi gurɓatattu kamar ƙone-ƙonen abubuwa masu guba, da kuma sare dazuka ko bishiyoyi. Waɗannan abubuwan suna sanya sinadaran iskoki masu riƙe zafi su yawaita, ana masu laƙabi da greenhouse gases. Yawaitar waɗannan iskoki suna sanya yanayi ya sauya ta hanyoyi kamar haka: 1. Yawan zafin yana iya kawo fari ta yanda ƙasa zata rasa danshi sakamakon rashin bishiyoyi. Hakan yana kawo ƙarancin kayan gona sakamakon rashin samun wadataccen ruwan dazai taimaka wajen noma. 2. Dalili na sama yana kaiwa ga taɓa lafiyar mutane, musamman ƙananan yara. Rashin wadatar iskar numfashi ta oxygen daga bishiyoyin da aka sare na iya kaiwa ga taɓa lafiyar ƙwaƙwalwa. 3. Yawaitar zafi kan iya ɗumama Duniyar baki ɗaya. Babban ƙalubalen anan shine narkewar manyan dusar ƙanƙara wanda hakan yake kawo am...

ZUCIYA (THE HEART)

Image
Zuciya tana ɗaya daga cikin tsoka mafi muhimmanci a jikin kowacce halitta; walau mutum ko dabba. Aikinta ya tattara ga samar da jini ga dukkanin sassan jiki ta hanyar wasu ɗakuna (chambers) guda huɗu, bututu da magudanai masu yawa. Waɗannan sune da alhakin samar da iskar numfashi (oxygen) tattare da sinadaran gina-jiki sun isa kowanne yanki a jiki. A yau, wannan kashin na KUNDIN SCIENCE IN HAUSA zai tattauna siffa da aikin kowane sashe na zuciya ne. Ɗakunan Zuciya Zuciya tana ɗauke da ɗakuna huɗu, waɗanda biyu suke a sama masu suna suna atrium ta dama da kuma atrium ta hagu. Sai kuma ɗakunan ƙasa guda biyu: ventricle ɗin dama, da kuma ventricle ɗin hagu. Atrium ta dama shine da alhakin karɓar jini wanda bai gauraya da iskar numfashi ba domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin dama da yake ƙasa. Atrium ta hagu kuma aikinta karɓar jinin daya gauraya da iskar numfashi domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin hagu. Amfanin ɗakunan ventricles shine fitar da jini daga cikin zuciya. Bututun Zuciya Zu...

CIWON DAJI (Cancer)

Image
CIWON DAJI (CANCER) Ciwon daji (Turanci: Cancer) wani launin ciwone wanda yake samuwa sakamakon waɗansu dalilai da ilmin Kimiyya yake ta ƙoƙarin zaƙulo su kullum. Cutar daji tana daga cikin manyan cututtuka da Duniya take fama dasu a yanzu saboda sarƙaƙiyar dake tattare da magance cutar. A kiyasi, ɗaya cikin bakwai na kowacce mutuwa a Duniya ana samun mai cutar daji a ciki; misali kamar cutar daji ta huhu, nono, hanji da kuma sauransu. Jikin ɗan Adam tattare yake da ƙwayoyin halittu kimanin biyalin sau dubu wadanda idan suka samu matsala suke komawa gyambon cutar daji. Wadannan ƙwayoyin halittu sun haɗa da; 1- Epithelial: Waɗannan ƙwayoyin halittu sune suke kawo cutar daji a fatar mutum da kashi 80 zuwa 90. 2- Magamar Matattara (Connective Tissue): Wannan cutar ta daji itace wacce take shafar kayan ciki kamar 'yayan hanji, baki da mara. 3- Jini Da Ɓargo (Blood & Lymphatic): Wannan tana daga cikin mafi munin cutukan daji. Ƙwayoyin halittu na jini wadanda suka samu ma...