Bikin Baje Kolin HIBAF 2025
Taken bikin na wannan shekarar shi ne "Rumbunan Ilimi," wanda zai yi duba izuwa ga tushe da tsarin ilimin Hausawa tun kafin zuwan Musulunci, Larabawa da kuma Turawan Mulkin-mallaka. Bikin na wannan shekarar zai karkata ne ga tarin fasahohin Hausawa a fannonin rayuwa a da da kuma yanzu ta hanyar gayyato masana, gwaje-gwaje, da sauransu.
Bikin HIBAF ba wai ga Arewacin Najeriya ya tsaya ba kaÉ—ai, a'a; taro ne da yake samun halartar mutane daga sassa na Duniya. Kama daga Hausawa, da kuma masu sha'awar nazarin harshen Hausa da al'adun su.
A yayin bitar bikin wanda ya gudana a harabar Open Arts ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi, Sada Malumfashi, da kuma Salma Ja'eh, an yi tsokaci akan yanda taron zai kasance cikin ƙayatarwa da nishaɗi. Taron zai samu baƙoncin malamai, mawaƙan baka, da kuma masu wasanni.
Farfesa Malumfashi ya daɗa yin tsokaci akan yanda bikin zai ƙayatar ta fuskar bayyana wasu ilmuka da suka shuɗe a cikin ƙasar Hausa. Hakan yana nuni da irin tarin tagomashin da taron wannan shekarar zai zo da shi. Ciki har da fasahohin kimiyya da ƙere-ƙere a sana'o'in Hausawa.
Taron zai gudana ne a ranakun 18 zuwa 20 na watan Disambar 2025 a babban É—akin taro na Arewa House a cikin birnin Kaduna. Har yanzu ana cigaba da rajistar bikin baje kolin wanda a yau saura makwanni biyu a fara gudanar da shi.
Za ku iya rajistar anan:
Mu haÉ—u a #HIBAF25
Kar ku manta har yanzu kafar yin rejista a buÉ—e ta ke: https://www.hausabaf.com/register
- El-Mubarak Jigirya
Babban Edita, Kundin Science In Hausa


Wannan Abu Yayi kyau
ReplyDeleteMadalla
Delete