Posts

Showing posts from May, 2022

TAKI (Fertilizer)

Image
  TAKI (Fertilizer) Tsirrai, shukoki da fure sukan samu nakasu yayin da suka gaza samun wadatattun abubuwan da zasu sanya su girma da lafiya. Taki (Turanci: Fertilizer) wani nau'in sinadari ne da yake sanya shuka girma da karko cikin kankanin lokaci; hakan, tareda karawa shukar kyau da lafiya. Sinadarai na taki sune suke taka muhimmiyar rawa a harkar nomar shuke-shuke. Taki ya kasu kashi biyu ta fannin abubuwan da suke cikinsa da kuma tasirinsa a jikin shuka. Wadannan takin sune; 1- Takin gida (Organic): Wannan takin shine wanda ake samu daga kashin dabbobi dana mutane. Galibi takin gida ya kunshi sinadarin carbon ne mai tarin yawa da kuma wadansu burbushi na wasu sinadaran. Akwai kuma dunkulen taki (composite) wanda yake samuwa daga matattun dabbobi, itatuwa da kuma sauran sinadaran da suke cikin kasa. Wannan launin taki yakan dauki tarin shekaru kafin ya samu: yakan samune idan matsi da zafi suka matse wadannan abubuwan dana lissafo a sama. Sukan dunkule bayan dogon lokaci, sanna