Sauyin Yanayi (Climate Change)


 Sauyin yanayi (Turanci: Climate Change) wani irin sauyi ne mai tasiri wanda ya shafi yanayin zafi, tsarukan damina, hunturu ko bazara a Duniya.


Waɗannan sauye-sauye suna samuwa ne saboda irin ayyukan da mutane sukeyi gurɓatattu kamar ƙone-ƙonen abubuwa masu guba, da kuma sare dazuka ko bishiyoyi.


Waɗannan abubuwan suna sanya sinadaran iskoki masu riƙe zafi su yawaita, ana masu laƙabi da greenhouse gases. Yawaitar waɗannan iskoki suna sanya yanayi ya sauya ta hanyoyi kamar haka:


1. Yawan zafin yana iya kawo fari ta yanda ƙasa zata rasa danshi sakamakon rashin bishiyoyi. Hakan yana kawo ƙarancin kayan gona sakamakon rashin samun wadataccen ruwan dazai taimaka wajen noma.


2. Dalili na sama yana kaiwa ga taɓa lafiyar mutane, musamman ƙananan yara. Rashin wadatar iskar numfashi ta oxygen daga bishiyoyin da aka sare na iya kaiwa ga taɓa lafiyar ƙwaƙwalwa.


3. Yawaitar zafi kan iya ɗumama Duniyar baki ɗaya. Babban ƙalubalen anan shine narkewar manyan dusar ƙanƙara wanda hakan yake kawo ambaliya, musamman ga yankunan da gaɓarsu take da manyan garuruwa.


A nahiyar Afirka, illolin sauyin yanayi suna yawaita ƙwararowar hamada, fari da kuma barazana ga lafiya da kuma dauka masu ɗauke da shukoki da dabbobi. Wannan kuwa yana taka muhimmiyar rawa wajen yawaitar talauci da sanya tsoro. 


Illolin sauyin yanayi suna da yawan gaske, kama daga abinda ya shafi noma, ruwa, lafiya, da kuma rayuwar dazuka da dabbobin cikinsu. Shiyasa gwamnatocin Duniya suka ɗauki ragamar samar da dokokin da zasu taimaka wajen kiyaye muhalli.

Mubarak Muhammad Salisu 

28 Disamba, 2023


Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki