FATA (The Skin): Kashi Na II

 SCIENCE IN HAUSA: Episode 4 (Part 2)

Fata (The Skin)


Hypodermis (fatar kasa) itace dauke da kitse. Wannan kitsen shine yake samar da sinadarin leptin; sinadarin dake kai sako kwakwalwa idan mutum ya kamu da yunwa. Har wa yau kitsen cikin dermis shine yake sanya jin dadi yayinda mutum ya kishingida a jikin abu mara taushi. Cikin hypodermis ake samun kwayoyin macrophages wadanda suke da alhakin kashe cutar da ta wuce epidermis da dermis. Macrophages suna samuwa ne daga cikin bargon kasusuwan dan Adam wato bone marrow.


Yayinda mutum ya kamu da sanyi sai receptors dinsa su amsa ta yanda gashin jikinsa zasu mike (erector pili) sannan jijiyoyin jininsa zasu matse ya samu dumi. Idan kuma yana jin zafi sai su bude ta yanda iska zata samu cikin sauki. Idan mutum yaji ciwo akwai kwayoyin halittu na fibroblasts wadanda sune ke kafar da jini ta hanyar clotting sannan su dinga samar da fata marar kauri wacce zata rufe ciwon; shiyasa fatar kan gyambo batada launi irin na sauran jiki.


Yayin da mutum yayi aiki na motsa jiki sai kofofin gashin su bude gumi ya fito. Wannan gumin yana samuwane daga sebaceous glands; haduwar gumin da kwayoyin bacteria ke kawo sauyin kamshi a jikin dan Adam.


A takaice wannan shine yanda fatarmu take aiki cikin ikon Ubangiji. Ina matukar godiya da yanda kuke bayar da goyan bayanku da shawarwari.


© Mubarak MS Jigirya

      10/07/2021

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

ÆŠakika Guda Ta Falaki

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)