SCIENCE IN HAUSA

 SCIENCE IN HAUSA: Bambanci tsakanin GUBA (Poison) da DAFI (Venom).


Guba (poison) da Dafi (venom) suna daga cikin dangin gurbatattun sinadarai (toxins) wadanda suke sauya akalar garkuwar jikin dan Adam ta hanyar cutarwa. Lokuta da dama daliban ilmi sukan samu rashin fahimtar yanda wadannan abubuwan suke. Nayi kokari wajen bayyana hakan cikin wannan rubutun.


1- DAFI (Venom): Wannan sinadarin ana samunsa ne daga halittu masu sara ko harbi, kamar macizai, gizagizo, kudan zuma ko shanshani. Dafi yana dauke da sinadarin PEPTIDES da/ko kuma da PROTEINS. Yana shiga jikin halitta ne ta hanyar cizo ko harbi daga cikin halittun dana ambata a sama. Wannan dafin yana bin hanyoyin jini ya toshesu ta hanyar rage gudun jinin ko kuma ya narkar da  kayan cikin wasu halittun; wannan yana faruwa ne idan halittar da tayi cizon ko harbin bata iya hadiye abinci mai tauri. Dafin saiya narkar da kayan cikin halittar da aka harba ta yanda za'a iya zuke abinda yake cikinta cikin sauki.


A kiyasi na kimiyya, akwai adadin dangin halittu masu dafi daban-daban kimanin 250,000 a Duniya. Ana kuma samunsu a kowacce nahiya ta Duniya face a yankin Antarctica. Dafi baya tasiri mai tsanani idan aka hadiya ta baki saboda karfin sinadarin acid din cikin dan Adam yana iya narkar da peptides da proteins din cikinsa.


Halittu mafiya yawan dafi a Duniya sun hada da kumurci (cobra), black mamba, viper, bakin gizagizo (black widow), da kuma maciji mafi dafi a Duniya wato inland taipen na kasar Australia. Wasu dafin akanyi amfani dasu wajen magance cututtuka kamar ciwon daji (cancer) da ciwon zuciya (cardiovascular diseases).


2- GUBA (Poison): Guba ana samunta ne a jikin halittu wadanda basa harbi ko sara kamar kwado ko kuma tsirrai wadanda sukeda gurbatattun sinadarai a jikinsu. Guba tana daukene da sinadarin ALKALOIDS wadanda sukeda karfi matuka idan suka shiga jikin halitta. Guba tana shiga jikin halitta ne ta hanyar hadiya, sha ko kuma tsotsewa ta jikin fata.


Halittun da sukeda guba suna samun gubar ne daga tsirrai ko kuma wadansu abubuwan masu dauke da gubar. Mafi akasari halitta tana samun gubane ta hanyoyin dana zayyano a sama bawai ta hanyar harbi ba.


A hasashen masu ilmin kimiyya, guba tana iya fin dafi hatsari saboda saurin tasirinta wajen karyar garkuwar jiki cikin kankanin lokaci.


A karshe... Halittu masu dafi suna dauke da dafine a kashi 50 na nauyin jikinsu. Sannan halittu masu guba basuda yawan halittu masu dafi.


© Mubarak MS Jigirya

     May 26, 2021

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

ÆŠakika Guda Ta Falaki

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)