KAREN RUWA (TARDIGRADE)

 SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU

KASHI NA BIYU (Episode 2)

A cikin tarin halittu da suke wanzuwa cikin wannan duniyar tamu, mukan kasasu izuwa sashe daban-daban ta fuskar dabi'u, siffa ko yanayin cima. Mukan dauki zaki a mafi kwarjini, giwa mafi karfi, dila mafi wayo da sauransu... Dakata! Amma duk hakan ba abun mamaki bane idan kasan halittar TARDIGRADE; halitta mai dumbin al'ajabi da bayananta zasu zo kamar tatsuniya.


Karen Ruwa (Turanci: Tardigrade) mai sunan kimiyya "Echiniscus succineus" wani irin launin halitta ne mai kankanta fiye da sauro da kafafu har takwas. Karen ruwa yanada tsawo kimanin milimita guda (1 millimeter) da kuma nauyi wanda bashida muhimmanci sosai. Yana daga cikin dangin halittu da akewa lakabi da "microorganisms"; ma'ana wadanda idanu basa iya gani saboda kankanta. A kiyasi na binciken malaman kimiyya, akwai akalla dangin karen ruwa kimanin 1100 da aka sani.


Daga cikin abubuwa mafi mamaki gameda wannan halitta shine yanda take iya rayuwa a wurare mafi tsauri kamar;

- Tsananin sanyi kasa da awon da sauran halittu zasu iya rayuwa; -272°C kamar a yankin Arctic Circle ko nahiyar Antarctica.


- Zafi mai kuna fiye dana tafasasshen ruwan zafi a ma'aunin 150°C; wannan ya hada harda iya wanzuwa cikin ko kusa da duwatsu masu aman wuta.


- Karfaffan zafi (radiation): wannan ya hada da wuraren mafiya gubar kwayoyin zafi. Wani abun al'ajabi shine iya wanzuwar karen ruwa a wajen duniya (outer space) ba tareda ya mutu ba saboda taurin ransa.


Hakazalika, wadannan halittu sun shahara wajen iya rayuwa ba tareda ruwa ba. Mai karatu zaiyi mamakin jin hakan amma babu mamaki a halittar da zata iya dakatar da numfashinta da girmanta; sunayin hakan ne ta hanyar dakatar da komai nasu (suspended animation). Wadannan halittu kan zauna a hakane tareda zagaye kwayoyin halittunsu (cells/molecules) da wani lullubi dazai hana komai motsawa kamar irinsu kwayoyin bayanai (DNA), sinadaran gina jiki (proteins) da sauransu. Haka zasu kasance har izuwa lokacin da ruwa zai samu; sukan kai shekaru talatin a hakan ba tareda sun mutu ba. Ana yiwa wannan yanayin lakabi da "anhydrobiosis"; wato rayuwa ba tareda danshi ko ruwa ba.


Wadannan halittu ana samunsu a saman ko jikin duwatsu, koramu ko tekuna, lambuna ko jikin itatuwa. Sukan wanzu tsawon lokaci kuma sune ake kallo a matsayin halittu mafiya karfi saboda irin dabi'unsu da suka sabawa sauran halittu wajen rayuwa.


Ina jaddada godiya gareku da irin hakurin da kukeyi wajen bibiyar shafina da ayyukana domin daukaka kimiyya a cikin harshenmu mai albarka, wato Hausa.


Na gode.


©Mubarak MS Jigirya

27/11/2021

Comments

  1. Allah mai girma!
    Allah buwayi gagara misali, gaskiya wannan halitta dauke take da ababan mamaki. Mallam Allah ya kara basira

    ReplyDelete
  2. Wani abu Sai ikon Allah kankanta Kamar sauro Kuma zasu iya rayuwa cikin Koh wani yanayi🤔

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki