SARARIN SATURN (Planet Saturn)

 SCIENCE IN HAUSA: Babi Na 2

Kashi Na 5


SCIENCE IN HAUSA 📚💡: SARARIN SATURN (Planet Saturn)

Falakinmu cike yake da ababan al'ajabi, kama daga tarin bangorai masu yawo cikin sarari da kuma duniyoyi har guda takwas da suke zagaye rana. Daya daga cikin wadannan duniyoyin itace Saturn: ta biyu a mafi girma bayan Jupiter. Wannan kashin zamu tattauna ne akan sararin Saturn.

Sararin Saturn itace ta biyu a mafi girma: da za'a ce a jera duniyar nan tamu a cikinta, sai an jera guda goma a mike kafin su kure tsawonta. Tanada launin ruwan zinare saboda irin sanadaran da suke cikinta kamar iskoki, narkakkun sinadarai da kuma sinadarin ammonia mai launin lu'u-lu'u. Wadannan iskokin sune na hydrogen da helium wadanda sune da mafi rinjaye na gaba daya nauyin sararin; kama daga gajimare har zuwa doron kasa. Hakanne yasa babu cikakkiyar turbaya a Saturn saboda tarin wadannan iskoki da suka sanya sararin batada nauyi.

Zakuyi mamaki idan nace koda za'a samu teku mai fadin dazai iya daukar Saturn, to bazata nutse ba. Kafin kuce a'ah zanso mu leka cikin kundun/cibiyar Saturn din wacce take tattare da ruwa, kankara da kuma duwatsu kadai. Wannan ya saba da sauran sararin, musamman ma wannan duniyar tamu da kundunta na bakin karfene. Wannan dalilin yasa ruwa ma yafi Saturn din nauyi.

Sararin Saturn dauke take da watanni da suke zagayata daidai har guda 50 (a iya sanin masana kenan). Abun mamakin shine yanda wadannan tarin watanni suke zagaya wannan sararin ta gurare mabambanta daga ciki da wajenta. Mafi girma a cikin watannin shine Titan: yanada girma daidai da kasar Canada da misalin fadin mil 3,200. Mafi kankanta shine Enceladus mai girma daidai da jihar Pennsylvania ta kasar Amurka. A hasashen kimiyya, Enceladus zai iya daukar halittu masu rai saboda kankarar dake kansa wacce zata iya narkewa izuwa narkakken ruwa. Sauran watannin sun hada da;

- Iapetus

- Rhea

- Dione

- Tethys; da kuma,

- Mimas

Lura: Wadannan suna kadan daga cikin wadanda aka sanyawa suna.

Wani babban kuma kebabben al'amari da Saturn shine zoben dake zagaye sararin. Wannan zuben ya samo asaline daga bangorai, watanni da kuma taurari masu wutsiya da suka ragargaje sannan karfin majanyar Saturn din ta janyosu izuwa sararin. Wannan zoben yanada matakai har bakwai masu kamanceceniya. A kauli mafi rinjaye na masana kimiyya, sararin Saturn itace garkuwa ga sauran sararin cikin falakinmu wadanda suke gaban Damarar Asteroid. Tana karesu daga manyan bangorai daka iya yi masu illa ko kuma jirkicesu daga bisa kawanyoyinsu.

Wannan kadan kenan daga cikin tarin bayanan sararin Saturn. Ina matukar godiya da goyan bayanku gareni da kuma shawarwari masu amfani. Na gode.

© Mubarak MS Jigirya

29/01/2022

Comments

Popular posts from this blog

ZUCIYA (THE HEART)

CIWON DAJI (Cancer)

Ɗakika Guda Ta Falaki