Posts

Showing posts from December, 2025

Bikin Baje Kolin HIBAF 2025

Image
  Bikin Baje Koli Da Fasahohin Hausawa wani taro ne da yake gudana a kowacce shekara a Æ™arÆ™ashin Gidauniyar Open Arts. Bikin wanda ake yiwa laÆ™abi da HIBAF (Hausa International Book and Arts Festival) yana bayyana al'adun Hausawa ne ta hanyoyi mabambanta da suka haÉ—a da adabi, waÆ™oÆ™in baka da na zube, tattaunawa ta ga-mu-ga-ku, wasannin kwaikwayo, da sauransu. Taken bikin na wannan shekarar shi ne "Rumbunan Ilimi," wanda zai yi duba izuwa ga tushe da tsarin ilimin Hausawa tun kafin zuwan Musulunci, Larabawa da kuma Turawan Mulkin-mallaka. Bikin na wannan shekarar zai karkata ne ga tarin fasahohin Hausawa a fannonin rayuwa a da da kuma yanzu ta hanyar gayyato masana, gwaje-gwaje, da sauransu. Bikin HIBAF ba wai ga Arewacin Najeriya ya tsaya ba kaÉ—ai, a'a; taro ne da yake samun halartar mutane daga sassa na Duniya. Kama daga Hausawa, da kuma masu sha'awar nazarin harshen Hausa da al'adun su. A yayin bitar bikin wanda ya gudana a harabar Open Arts Æ™arÆ™ashin jagor...