Posts

KWARKWATAR KIFI (Cymothoa exigua)

Image
 SCIENCE IN HAUSA πŸ“šπŸ’‘ Daga cikin tarin halittun da basuda iyaka a wannan sararin na duniya, akwai masu amfani kamar kananun halittu masu taimakawa dan Adam narkar da sinadarai (enzymes); sannan kuma akwai masu zama a jikin sauran halittu (Parasite). Wadannan halittun sukan cutar ko kuma su taimakawa halittar da suke zama jikinta; daya daga cikinsu shine/itace Kwarkwatar Kifi. Kwarkwatar Kifi (Turanci: Cymothoa exigua) wata karamar halitta ce da take zama a cikin teku, sannan kuma kwarin mannau ne (parasite) da suke zama a cikin kifaye. Wannan halitta tana daga cikin halittu masu kaurin fatar jiki (crustacean); launin Athropoda; sannan kuma zuri'ar Malacostraca. Wadannan halittu kuma kamar kwarkwata suke (louse) saboda dabi'ar ciyarwa ta hanyar tsotsan jini. Babban abun al'ajabi ga Kwarkwatar kifin shine: sunada dabi'ar sauya jinsi daga namiji zuwa mace saboda wanzuwar al'aurorin mace da namiji a tattare dasu. Ana masu lakabi da "Protoandritic Hermaphrodite...

SARARIN SATURN (Planet Saturn)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: Babi Na 2 Kashi Na 5 SCIENCE IN HAUSA πŸ“šπŸ’‘: SARARIN SATURN (Planet Saturn) Falakinmu cike yake da ababan al'ajabi, kama daga tarin bangorai masu yawo cikin sarari da kuma duniyoyi har guda takwas da suke zagaye rana. Daya daga cikin wadannan duniyoyin itace Saturn: ta biyu a mafi girma bayan Jupiter. Wannan kashin zamu tattauna ne akan sararin Saturn. Sararin Saturn itace ta biyu a mafi girma: da za'a ce a jera duniyar nan tamu a cikinta, sai an jera guda goma a mike kafin su kure tsawonta. Tanada launin ruwan zinare saboda irin sanadaran da suke cikinta kamar iskoki, narkakkun sinadarai da kuma sinadarin ammonia mai launin lu'u-lu'u. Wadannan iskokin sune na hydrogen da helium wadanda sune da mafi rinjaye na gaba daya nauyin sararin; kama daga gajimare har zuwa doron kasa. Hakanne yasa babu cikakkiyar turbaya a Saturn saboda tarin wadannan iskoki da suka sanya sararin batada nauyi. Zakuyi mamaki idan nace koda za'a samu teku mai fadin dazai iya d...

TSATSA (RUSTING)

Image
  SCIENCE IN HAUSA πŸ“šπŸ’‘: TSATSA (RUSTING) KASHI NA MUSAMMAN Abubuwa da dama sukan lalace tsawon lokaci bayan kirkirarsu; walau su rube, ko su dagargaje, ko su kece/yage ko kuma subi iska. Karafa sukan lalace ta hanyar yin wani abu mai suna tsatsa. A wannan karon zamu tattauna ne akan yanda karafa sukan lalace da dalilan yin hakan. Tsatsa (Turanci: Rusting) wani irin nau'ine na rubewa da yake shafar wadansu daga cikin karafa. Abinda yasa nace wasu shine; duk da tarin karafa da muka sani, ba kowanne bane yakeyin tsatsa. Wannan ya ta'allaka ne da dabi'un kwayoyin zarrar cikin kowanne karfe. (Duba kashi akan "Kwayar Zarra" domin karin bayani).  Tsatsa tafi shafar bakin karfe wato Iron (Fe) saboda karfin sauyawarsa yayin daya hadu da wasu burbushin sinadarai. Wannan nau'in lalacewa na bakin karfe (Fe) yana faruwa ne yayin da kwayoyin zarrarsa suka hadu dana iskar oxygen (O2) da kuma ruwa (H2O): ana yiwa wannan hadaka lakabi da "redox reaction" wacce a Hau...

DAMARAR KUIPER (KUIPER BELT)

Image
SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU KASHI NA UKU (EPISODE 3) A baya mun samu bayanai akan Damarar Asteroid wacce ta yiwa falakinmu kawanya ta ciki daga gaban Duniyar Neptune. Mun tattauna gameda ire-iren abubuwan da suke cikin kawanyar da sauransu. A yau ma kamar wancan lokacin, zamuyi ninkaya ne domin cimma wata damarar wacce itace ta biyu a cikin falakinmu na Milky Way. Damarar Kuiper (Turanci: Kuiper Belt) wani yankine a sararin samaniya wanda shine ake yiwa hasashen karshen falakinmu ta fuskar abubuwan da ido zaya iya gani. Damarar Kuiper tana somawa ne daga bayan duniyar Neptune ta kewaye dukkan falakin kamar zobe: ana wannan yanki lakabi da "Outer Planets", wato duniyoyin waje. Nisan Damarar Kuiper zuwa rana daidai yake da 50AU (Astronomical Unit): wato wani nau'in ma'auni na ilmin taurari wanda yake daidai da tafiyar mil 93,498,125 sau 50; AU guda shine tazarar duniyar da muke ciki zuwa rana. Hakan shine nisan daya raba Damarar Kuiper da Ranar Falakinmu.  Damarar As...

KAREN RUWA (TARDIGRADE)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU KASHI NA BIYU (Episode 2) A cikin tarin halittu da suke wanzuwa cikin wannan duniyar tamu, mukan kasasu izuwa sashe daban-daban ta fuskar dabi'u, siffa ko yanayin cima. Mukan dauki zaki a mafi kwarjini, giwa mafi karfi, dila mafi wayo da sauransu... Dakata! Amma duk hakan ba abun mamaki bane idan kasan halittar TARDIGRADE; halitta mai dumbin al'ajabi da bayananta zasu zo kamar tatsuniya. Karen Ruwa (Turanci: Tardigrade) mai sunan kimiyya "Echiniscus succineus" wani irin launin halitta ne mai kankanta fiye da sauro da kafafu har takwas. Karen ruwa yanada tsawo kimanin milimita guda (1 millimeter) da kuma nauyi wanda bashida muhimmanci sosai. Yana daga cikin dangin halittu da akewa lakabi da "microorganisms"; ma'ana wadanda idanu basa iya gani saboda kankanta. A kiyasi na binciken malaman kimiyya, akwai akalla dangin karen ruwa kimanin 1100 da aka sani. Daga cikin abubuwa mafi mamaki gameda wannan halitta shine yanda take iy...