Posts

CUTAR DAJIN FARJI (Vaginal Cancer)

Image
KUNDIN SCIENCE IN: Tsokaci Maudu'i: Cutar Dajin Farji (Vaginal Cancer) Kwanakin baya nayi bayani akan cutar dajin Æ™ashi (leukaemia); haÉ—e da jawabin yanda take samuwa da maganinta. Kafin wannan nayi kuma akan cutar dajin mama (breast cancer). Cikin 'yan kwanakin nan nayita samun tambayoyi gameda cutar dajin farji, musamman daga É—aliban ilmi. To a gurguje inason nayi bayani akan ita cutar dajin farji.  Kamar yanda nayi jawabi a lakcocin baya: cutar daji tana samuwa ne daga gurÉ“atattun Æ™wayoyin halittun da basu mutu ba a cikin jikin É—an Adam. WaÉ—annan gurÉ“atattun Æ™wayoyin halittun suna iya kama kowanne É“angare a jikin mutum idan suka fara yawaita. Cutar dajin farji tana kama matane a cikin farjinsu ta hanyar farawa da samar da gyambo (tumour) kafin ta nuna kanta. Akwai waÉ—ansu abubuwa daya kamata mace ta lura dasu; idan tana ganin yawaita afkuwarsu, ta tuntuÉ“i likita: 1- Fitsari haÉ—e da jini. 2- Fitar ruwa daga gabanta. 3- Yawaitar sauyin É—anÉ—ano a baki. 4- Kumburin m...

CUTAR DAJIN ƘASHI (Leukaemia)

Image
Cutar daji (Turanci: Cancer) wani nau'in ciwone da yake samuwa daga kwayoyin halittu (cells) na jikin dan Adam; wala'alla saboda nakasa da suka samu ko kuma gurbacewa daga sinadarai masu guba. Wannan cuta ta kasu izuwa kashi akalla guda dari daya: daga kan cutar daji ta kwakwalwa, hanta, mama (nono), makogaro, da sauransu. Leukaemia tana daya daga cikin nau'o'in cutar daji wadda tafi kama yara 'yan kasa da shekara goma sha biyar. Wannan cutar daji ana mata lakabi da "cancer of the bone"; wato cutar dajin Æ™ashi saboda ta samo asaline daga cikin Æ™ashin mutane da kuma É“argon jikinsu.  Cutar dajin Æ™ashi tana farawa ne a yayin da aka samu tangarÉ—a wajen samar da kwayoyin halittu. Wadannan kwayoyin halittu suna farawa ne a matsayin jirajirai (stem cells) a cikin É“argon Æ™ashin kafin su girma su samawa kansu gurbi a cikin tsokoki da dama kamar hanta, zuciya da Æ™oda. Wadannan kwayoyin halittu da suke samuwa daga cikin É“argon Æ™ashi sun hada da: - Jajayen...

TAKI (Fertilizer)

Image
  TAKI (Fertilizer) Tsirrai, shukoki da fure sukan samu nakasu yayin da suka gaza samun wadatattun abubuwan da zasu sanya su girma da lafiya. Taki (Turanci: Fertilizer) wani nau'in sinadari ne da yake sanya shuka girma da karko cikin kankanin lokaci; hakan, tareda karawa shukar kyau da lafiya. Sinadarai na taki sune suke taka muhimmiyar rawa a harkar nomar shuke-shuke. Taki ya kasu kashi biyu ta fannin abubuwan da suke cikinsa da kuma tasirinsa a jikin shuka. Wadannan takin sune; 1- Takin gida (Organic): Wannan takin shine wanda ake samu daga kashin dabbobi dana mutane. Galibi takin gida ya kunshi sinadarin carbon ne mai tarin yawa da kuma wadansu burbushi na wasu sinadaran. Akwai kuma dunkulen taki (composite) wanda yake samuwa daga matattun dabbobi, itatuwa da kuma sauran sinadaran da suke cikin kasa. Wannan launin taki yakan dauki tarin shekaru kafin ya samu: yakan samune idan matsi da zafi suka matse wadannan abubuwan dana lissafo a sama. Sukan dunkule bayan dogon lokaci, sanna...

KWARKWATAR KIFI (Cymothoa exigua)

Image
 SCIENCE IN HAUSA 📚💡 Daga cikin tarin halittun da basuda iyaka a wannan sararin na duniya, akwai masu amfani kamar kananun halittu masu taimakawa dan Adam narkar da sinadarai (enzymes); sannan kuma akwai masu zama a jikin sauran halittu (Parasite). Wadannan halittun sukan cutar ko kuma su taimakawa halittar da suke zama jikinta; daya daga cikinsu shine/itace Kwarkwatar Kifi. Kwarkwatar Kifi (Turanci: Cymothoa exigua) wata karamar halitta ce da take zama a cikin teku, sannan kuma kwarin mannau ne (parasite) da suke zama a cikin kifaye. Wannan halitta tana daga cikin halittu masu kaurin fatar jiki (crustacean); launin Athropoda; sannan kuma zuri'ar Malacostraca. Wadannan halittu kuma kamar kwarkwata suke (louse) saboda dabi'ar ciyarwa ta hanyar tsotsan jini. Babban abun al'ajabi ga Kwarkwatar kifin shine: sunada dabi'ar sauya jinsi daga namiji zuwa mace saboda wanzuwar al'aurorin mace da namiji a tattare dasu. Ana masu lakabi da "Protoandritic Hermaphrodite...

SARARIN SATURN (Planet Saturn)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: Babi Na 2 Kashi Na 5 SCIENCE IN HAUSA 📚💡: SARARIN SATURN (Planet Saturn) Falakinmu cike yake da ababan al'ajabi, kama daga tarin bangorai masu yawo cikin sarari da kuma duniyoyi har guda takwas da suke zagaye rana. Daya daga cikin wadannan duniyoyin itace Saturn: ta biyu a mafi girma bayan Jupiter. Wannan kashin zamu tattauna ne akan sararin Saturn. Sararin Saturn itace ta biyu a mafi girma: da za'a ce a jera duniyar nan tamu a cikinta, sai an jera guda goma a mike kafin su kure tsawonta. Tanada launin ruwan zinare saboda irin sanadaran da suke cikinta kamar iskoki, narkakkun sinadarai da kuma sinadarin ammonia mai launin lu'u-lu'u. Wadannan iskokin sune na hydrogen da helium wadanda sune da mafi rinjaye na gaba daya nauyin sararin; kama daga gajimare har zuwa doron kasa. Hakanne yasa babu cikakkiyar turbaya a Saturn saboda tarin wadannan iskoki da suka sanya sararin batada nauyi. Zakuyi mamaki idan nace koda za'a samu teku mai fadin dazai iya d...