Posts

Bikin Baje Kolin HIBAF 2025

Image
  Bikin Baje Koli Da Fasahohin Hausawa wani taro ne da yake gudana a kowacce shekara a ƙarƙashin Gidauniyar Open Arts. Bikin wanda ake yiwa laƙabi da HIBAF (Hausa International Book and Arts Festival) yana bayyana al'adun Hausawa ne ta hanyoyi mabambanta da suka haɗa da adabi, waƙoƙin baka da na zube, tattaunawa ta ga-mu-ga-ku, wasannin kwaikwayo, da sauransu. Taken bikin na wannan shekarar shi ne "Rumbunan Ilimi," wanda zai yi duba izuwa ga tushe da tsarin ilimin Hausawa tun kafin zuwan Musulunci, Larabawa da kuma Turawan Mulkin-mallaka. Bikin na wannan shekarar zai karkata ne ga tarin fasahohin Hausawa a fannonin rayuwa a da da kuma yanzu ta hanyar gayyato masana, gwaje-gwaje, da sauransu. Bikin HIBAF ba wai ga Arewacin Najeriya ya tsaya ba kaɗai, a'a; taro ne da yake samun halartar mutane daga sassa na Duniya. Kama daga Hausawa, da kuma masu sha'awar nazarin harshen Hausa da al'adun su. A yayin bitar bikin wanda ya gudana a harabar Open Arts ƙarƙashin jagor...

AMFANIN SUKARIN GLUCOSE

Image
  AMFANIN SUKARIN GLUCOSE Glucose nau'in sukari ne da ake yiwa laƙabi da "monosaccharide," wato dangin sukari mai rukuni ƙwayar zarra (molecule) ɗaya. Daga cikin wannan dangi akwai irinsu galactose da fructose, waɗanda sune suke haɗuwa su samar da cikakken sukari mai rukunin ƙwayar zarra biyu, wato "disaccharide." Dukannin wani nau'in sukari yana samuwa ne daga dangin abinci na carbohydrates, wato launukan abinci masu samar da kuzari da gina jiki irinsu shinkafa, dankali, gwaza, masara, da sauransu. Su kuwa waɗannan dangin abinci ɗauke suke da sinadaran hydrogen, carbon, da oxygen. Amfanin glucose a jiki ya haɗa da: 1. Samar da kuzari ga dukkanin ƙwayoyin halitta a jiki, wato cells. 2. Taimakawa ƙwaƙwalwa wajen gudanar da aiki cikin sauƙi. 3. Yaƙar cutukan ƙwaƙwalwa kamar Alzheimer da Parkinson. 4. Samar da lafiyar fata ta fuskar wadatar danshi da kore tamoji. 5. Ƙarawa ƙasusuwan jiki ƙwari, da kuma taimaka masu wajen gudanar aikin ƙarfi. 6. Glucose na taima...

Sauyin Yanayi (Climate Change)

Image
 Sauyin yanayi (Turanci: Climate Change) wani irin sauyi ne mai tasiri wanda ya shafi yanayin zafi, tsarukan damina, hunturu ko bazara a Duniya. Waɗannan sauye-sauye suna samuwa ne saboda irin ayyukan da mutane sukeyi gurɓatattu kamar ƙone-ƙonen abubuwa masu guba, da kuma sare dazuka ko bishiyoyi. Waɗannan abubuwan suna sanya sinadaran iskoki masu riƙe zafi su yawaita, ana masu laƙabi da greenhouse gases. Yawaitar waɗannan iskoki suna sanya yanayi ya sauya ta hanyoyi kamar haka: 1. Yawan zafin yana iya kawo fari ta yanda ƙasa zata rasa danshi sakamakon rashin bishiyoyi. Hakan yana kawo ƙarancin kayan gona sakamakon rashin samun wadataccen ruwan dazai taimaka wajen noma. 2. Dalili na sama yana kaiwa ga taɓa lafiyar mutane, musamman ƙananan yara. Rashin wadatar iskar numfashi ta oxygen daga bishiyoyin da aka sare na iya kaiwa ga taɓa lafiyar ƙwaƙwalwa. 3. Yawaitar zafi kan iya ɗumama Duniyar baki ɗaya. Babban ƙalubalen anan shine narkewar manyan dusar ƙanƙara wanda hakan yake kawo am...

ZUCIYA (THE HEART)

Image
Zuciya tana ɗaya daga cikin tsoka mafi muhimmanci a jikin kowacce halitta; walau mutum ko dabba. Aikinta ya tattara ga samar da jini ga dukkanin sassan jiki ta hanyar wasu ɗakuna (chambers) guda huɗu, bututu da magudanai masu yawa. Waɗannan sune da alhakin samar da iskar numfashi (oxygen) tattare da sinadaran gina-jiki sun isa kowanne yanki a jiki. A yau, wannan kashin na KUNDIN SCIENCE IN HAUSA zai tattauna siffa da aikin kowane sashe na zuciya ne. Ɗakunan Zuciya Zuciya tana ɗauke da ɗakuna huɗu, waɗanda biyu suke a sama masu suna suna atrium ta dama da kuma atrium ta hagu. Sai kuma ɗakunan ƙasa guda biyu: ventricle ɗin dama, da kuma ventricle ɗin hagu. Atrium ta dama shine da alhakin karɓar jini wanda bai gauraya da iskar numfashi ba domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin dama da yake ƙasa. Atrium ta hagu kuma aikinta karɓar jinin daya gauraya da iskar numfashi domin tunkuɗashi izuwa ventricle ɗin hagu. Amfanin ɗakunan ventricles shine fitar da jini daga cikin zuciya. Bututun Zuciya Zu...

CIWON DAJI (Cancer)

Image
CIWON DAJI (CANCER) Ciwon daji (Turanci: Cancer) wani launin ciwone wanda yake samuwa sakamakon waɗansu dalilai da ilmin Kimiyya yake ta ƙoƙarin zaƙulo su kullum. Cutar daji tana daga cikin manyan cututtuka da Duniya take fama dasu a yanzu saboda sarƙaƙiyar dake tattare da magance cutar. A kiyasi, ɗaya cikin bakwai na kowacce mutuwa a Duniya ana samun mai cutar daji a ciki; misali kamar cutar daji ta huhu, nono, hanji da kuma sauransu. Jikin ɗan Adam tattare yake da ƙwayoyin halittu kimanin biyalin sau dubu wadanda idan suka samu matsala suke komawa gyambon cutar daji. Wadannan ƙwayoyin halittu sun haɗa da; 1- Epithelial: Waɗannan ƙwayoyin halittu sune suke kawo cutar daji a fatar mutum da kashi 80 zuwa 90. 2- Magamar Matattara (Connective Tissue): Wannan cutar ta daji itace wacce take shafar kayan ciki kamar 'yayan hanji, baki da mara. 3- Jini Da Ɓargo (Blood & Lymphatic): Wannan tana daga cikin mafi munin cutukan daji. Ƙwayoyin halittu na jini wadanda suka samu ma...

Ɗakika Guda Ta Falaki

Image
KUNDIN SCIENCE IN HAUSA Ɗaƙiƙa Guda Ta Falaki  Falaki (Turanci: Universe) cike yake da ababan al'ajabi, kama daga yawan duniyoyi (planets) da suke a warwatse, ɓangorai (asteroid ko comets), ɗamaru (Asteroid, Kuiper da Heliosphere), watanni na duniyoyi da kuma tarin taurari. Wannan Falakin namu kuma ɗayane daga cikin biliyoyin Falakan da suke waje. Idan ban manta na taɓa faɗa mana sunan namu Falakin, wato "Milky Way" a Turance. Wannan Falaki namu ya tara duniyoyi guda takwas, tareda sauran ƙananun duniyoyi da akewa laƙabi da "Dwarf Planets"; irinsu Pluto da makamantansu. To amma meye yake faruwa a kowacce daƙiƙa a cikin wannan Falaki? Masana kimiyyar ilmin falaki wato "Cosmologists" sunyi ittifaƙin cewa a kowacce daƙiƙa guda waɗansu abubuwa masu tarin al'ajabi suna faruwa a cikinsa, kamar: 1. Ana haihuwar taurari kimanin 3,180 a kowacce daƙiƙa. 2. Daga cikin taurarin da suke wanzuwa tsawon biliyoyin shekaru, guda 900 suna fashewa yayinda...

TSIBIRIN MACIZAI (Ilha De Queimada Grande)

Image
TSIBIRIN MACIZAI (ILHA DA QUEIMADA GRANDE) A cikin tarin wuraren da suke da haɗari a doron duniyar nan, mutum bazai iya ƙidayo guda uku ba ba tareda daya lissafo da Tsibirin Macizai ba. Kafin mai karatu yace yau nazo da zance kamar tatsuniya, zanso a biyoni a hankali a kashin yau na Kundin Science In Hausa. Tsibirin Macizai (Ilha Da Queimada Grande) wani yankine a kasar Brazil ta nahiyar Amurka ta Kudu wanda yake mai hatsarin gaske saboda halittun da suke cikinsa. Kimanin kilomita 33 daga birnin Sao Paulo shimfiɗe a cikin tekun Atlantic zaka tarar da wannan tsibirin mai ɗumbin mamaki.  Tsibirin Macizai ya samo sunansa ne daga tarin macizan cikinsa wanda adadinsu yakai 4000. Macizan da sukayi kaka-gida a wannan tsibirin sune Zinariyar Kububuwa (Turanci: Golden Lancehead Viper) wadanda sukeda launuka daga kore da kuma na ruwan dorawa. Wadannan macizai sunada matukar ƙarfin dafi sau biyar fiyeda sauran kububuwar da suke kan tudu. A hasashe na tarihi ance wai 'yan fashin te...

CUTAR DAJIN FARJI (Vaginal Cancer)

Image
KUNDIN SCIENCE IN: Tsokaci Maudu'i: Cutar Dajin Farji (Vaginal Cancer) Kwanakin baya nayi bayani akan cutar dajin ƙashi (leukaemia); haɗe da jawabin yanda take samuwa da maganinta. Kafin wannan nayi kuma akan cutar dajin mama (breast cancer). Cikin 'yan kwanakin nan nayita samun tambayoyi gameda cutar dajin farji, musamman daga ɗaliban ilmi. To a gurguje inason nayi bayani akan ita cutar dajin farji.  Kamar yanda nayi jawabi a lakcocin baya: cutar daji tana samuwa ne daga gurɓatattun ƙwayoyin halittun da basu mutu ba a cikin jikin ɗan Adam. Waɗannan gurɓatattun ƙwayoyin halittun suna iya kama kowanne ɓangare a jikin mutum idan suka fara yawaita. Cutar dajin farji tana kama matane a cikin farjinsu ta hanyar farawa da samar da gyambo (tumour) kafin ta nuna kanta. Akwai waɗansu abubuwa daya kamata mace ta lura dasu; idan tana ganin yawaita afkuwarsu, ta tuntuɓi likita: 1- Fitsari haɗe da jini. 2- Fitar ruwa daga gabanta. 3- Yawaitar sauyin ɗanɗano a baki. 4- Kumburin m...

CUTAR DAJIN ƘASHI (Leukaemia)

Image
Cutar daji (Turanci: Cancer) wani nau'in ciwone da yake samuwa daga kwayoyin halittu (cells) na jikin dan Adam; wala'alla saboda nakasa da suka samu ko kuma gurbacewa daga sinadarai masu guba. Wannan cuta ta kasu izuwa kashi akalla guda dari daya: daga kan cutar daji ta kwakwalwa, hanta, mama (nono), makogaro, da sauransu. Leukaemia tana daya daga cikin nau'o'in cutar daji wadda tafi kama yara 'yan kasa da shekara goma sha biyar. Wannan cutar daji ana mata lakabi da "cancer of the bone"; wato cutar dajin ƙashi saboda ta samo asaline daga cikin ƙashin mutane da kuma ɓargon jikinsu.  Cutar dajin ƙashi tana farawa ne a yayin da aka samu tangarɗa wajen samar da kwayoyin halittu. Wadannan kwayoyin halittu suna farawa ne a matsayin jirajirai (stem cells) a cikin ɓargon ƙashin kafin su girma su samawa kansu gurbi a cikin tsokoki da dama kamar hanta, zuciya da ƙoda. Wadannan kwayoyin halittu da suke samuwa daga cikin ɓargon ƙashi sun hada da: - Jajayen...

TAKI (Fertilizer)

Image
  TAKI (Fertilizer) Tsirrai, shukoki da fure sukan samu nakasu yayin da suka gaza samun wadatattun abubuwan da zasu sanya su girma da lafiya. Taki (Turanci: Fertilizer) wani nau'in sinadari ne da yake sanya shuka girma da karko cikin kankanin lokaci; hakan, tareda karawa shukar kyau da lafiya. Sinadarai na taki sune suke taka muhimmiyar rawa a harkar nomar shuke-shuke. Taki ya kasu kashi biyu ta fannin abubuwan da suke cikinsa da kuma tasirinsa a jikin shuka. Wadannan takin sune; 1- Takin gida (Organic): Wannan takin shine wanda ake samu daga kashin dabbobi dana mutane. Galibi takin gida ya kunshi sinadarin carbon ne mai tarin yawa da kuma wadansu burbushi na wasu sinadaran. Akwai kuma dunkulen taki (composite) wanda yake samuwa daga matattun dabbobi, itatuwa da kuma sauran sinadaran da suke cikin kasa. Wannan launin taki yakan dauki tarin shekaru kafin ya samu: yakan samune idan matsi da zafi suka matse wadannan abubuwan dana lissafo a sama. Sukan dunkule bayan dogon lokaci, sanna...

KWARKWATAR KIFI (Cymothoa exigua)

Image
 SCIENCE IN HAUSA 📚💡 Daga cikin tarin halittun da basuda iyaka a wannan sararin na duniya, akwai masu amfani kamar kananun halittu masu taimakawa dan Adam narkar da sinadarai (enzymes); sannan kuma akwai masu zama a jikin sauran halittu (Parasite). Wadannan halittun sukan cutar ko kuma su taimakawa halittar da suke zama jikinta; daya daga cikinsu shine/itace Kwarkwatar Kifi. Kwarkwatar Kifi (Turanci: Cymothoa exigua) wata karamar halitta ce da take zama a cikin teku, sannan kuma kwarin mannau ne (parasite) da suke zama a cikin kifaye. Wannan halitta tana daga cikin halittu masu kaurin fatar jiki (crustacean); launin Athropoda; sannan kuma zuri'ar Malacostraca. Wadannan halittu kuma kamar kwarkwata suke (louse) saboda dabi'ar ciyarwa ta hanyar tsotsan jini. Babban abun al'ajabi ga Kwarkwatar kifin shine: sunada dabi'ar sauya jinsi daga namiji zuwa mace saboda wanzuwar al'aurorin mace da namiji a tattare dasu. Ana masu lakabi da "Protoandritic Hermaphrodite...

SARARIN SATURN (Planet Saturn)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: Babi Na 2 Kashi Na 5 SCIENCE IN HAUSA 📚💡: SARARIN SATURN (Planet Saturn) Falakinmu cike yake da ababan al'ajabi, kama daga tarin bangorai masu yawo cikin sarari da kuma duniyoyi har guda takwas da suke zagaye rana. Daya daga cikin wadannan duniyoyin itace Saturn: ta biyu a mafi girma bayan Jupiter. Wannan kashin zamu tattauna ne akan sararin Saturn. Sararin Saturn itace ta biyu a mafi girma: da za'a ce a jera duniyar nan tamu a cikinta, sai an jera guda goma a mike kafin su kure tsawonta. Tanada launin ruwan zinare saboda irin sanadaran da suke cikinta kamar iskoki, narkakkun sinadarai da kuma sinadarin ammonia mai launin lu'u-lu'u. Wadannan iskokin sune na hydrogen da helium wadanda sune da mafi rinjaye na gaba daya nauyin sararin; kama daga gajimare har zuwa doron kasa. Hakanne yasa babu cikakkiyar turbaya a Saturn saboda tarin wadannan iskoki da suka sanya sararin batada nauyi. Zakuyi mamaki idan nace koda za'a samu teku mai fadin dazai iya d...

TSATSA (RUSTING)

Image
  SCIENCE IN HAUSA 📚💡: TSATSA (RUSTING) KASHI NA MUSAMMAN Abubuwa da dama sukan lalace tsawon lokaci bayan kirkirarsu; walau su rube, ko su dagargaje, ko su kece/yage ko kuma subi iska. Karafa sukan lalace ta hanyar yin wani abu mai suna tsatsa. A wannan karon zamu tattauna ne akan yanda karafa sukan lalace da dalilan yin hakan. Tsatsa (Turanci: Rusting) wani irin nau'ine na rubewa da yake shafar wadansu daga cikin karafa. Abinda yasa nace wasu shine; duk da tarin karafa da muka sani, ba kowanne bane yakeyin tsatsa. Wannan ya ta'allaka ne da dabi'un kwayoyin zarrar cikin kowanne karfe. (Duba kashi akan "Kwayar Zarra" domin karin bayani).  Tsatsa tafi shafar bakin karfe wato Iron (Fe) saboda karfin sauyawarsa yayin daya hadu da wasu burbushin sinadarai. Wannan nau'in lalacewa na bakin karfe (Fe) yana faruwa ne yayin da kwayoyin zarrarsa suka hadu dana iskar oxygen (O2) da kuma ruwa (H2O): ana yiwa wannan hadaka lakabi da "redox reaction" wacce a Hau...

DAMARAR KUIPER (KUIPER BELT)

Image
SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU KASHI NA UKU (EPISODE 3) A baya mun samu bayanai akan Damarar Asteroid wacce ta yiwa falakinmu kawanya ta ciki daga gaban Duniyar Neptune. Mun tattauna gameda ire-iren abubuwan da suke cikin kawanyar da sauransu. A yau ma kamar wancan lokacin, zamuyi ninkaya ne domin cimma wata damarar wacce itace ta biyu a cikin falakinmu na Milky Way. Damarar Kuiper (Turanci: Kuiper Belt) wani yankine a sararin samaniya wanda shine ake yiwa hasashen karshen falakinmu ta fuskar abubuwan da ido zaya iya gani. Damarar Kuiper tana somawa ne daga bayan duniyar Neptune ta kewaye dukkan falakin kamar zobe: ana wannan yanki lakabi da "Outer Planets", wato duniyoyin waje. Nisan Damarar Kuiper zuwa rana daidai yake da 50AU (Astronomical Unit): wato wani nau'in ma'auni na ilmin taurari wanda yake daidai da tafiyar mil 93,498,125 sau 50; AU guda shine tazarar duniyar da muke ciki zuwa rana. Hakan shine nisan daya raba Damarar Kuiper da Ranar Falakinmu.  Damarar As...

KAREN RUWA (TARDIGRADE)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: BABI NA BIYU KASHI NA BIYU (Episode 2) A cikin tarin halittu da suke wanzuwa cikin wannan duniyar tamu, mukan kasasu izuwa sashe daban-daban ta fuskar dabi'u, siffa ko yanayin cima. Mukan dauki zaki a mafi kwarjini, giwa mafi karfi, dila mafi wayo da sauransu... Dakata! Amma duk hakan ba abun mamaki bane idan kasan halittar TARDIGRADE; halitta mai dumbin al'ajabi da bayananta zasu zo kamar tatsuniya. Karen Ruwa (Turanci: Tardigrade) mai sunan kimiyya "Echiniscus succineus" wani irin launin halitta ne mai kankanta fiye da sauro da kafafu har takwas. Karen ruwa yanada tsawo kimanin milimita guda (1 millimeter) da kuma nauyi wanda bashida muhimmanci sosai. Yana daga cikin dangin halittu da akewa lakabi da "microorganisms"; ma'ana wadanda idanu basa iya gani saboda kankanta. A kiyasi na binciken malaman kimiyya, akwai akalla dangin karen ruwa kimanin 1100 da aka sani. Daga cikin abubuwa mafi mamaki gameda wannan halitta shine yanda take iy...

DANYEN MAI (Crude Oil)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 15 Mukan wayi gari da karar ababen hawa tattare da hayaki daga cikin magunarsu. Wannan hayakin ya kasu izuwa kaso daban daban bisa nau'in abinda kowacce na'ura walau ta mota, babur ko injin lantarki (generator) suke samarwa. Ko kuma irin wanda muke fitarwa daga madafa a cikin tukwanen gas ko murhun zamani mai aiki da kalanzir. Duk wadannan launin hayakin sun samo asaline daga wani bakin ruwa mai daraja da akewa lakabi da DANYEN MAI. Danyen mai (Turanci: Crude Oil) wani irin nau'ine na ruwa mai launin baki da ake hakowa daga karkashin kasa; walau akan tsandauri ko kuma ta karkashin ruwan teku. A kiyasi na ilmin kimiyya, danyen mai ya samu ne daga matattun halittun ruwa (marine life) da suka dade da mutuwa milyoyin shekaru a baya. Wadannan matattun halittu sun narkene izuwa danyen mai bayan matsi da kuma narkon zafi daya motsesu tsawon lokaci. Tsawon lokaci, danyen mai ya zamto a kwance ne tsakanin duwatsu wadanda basa barin ruwa ya ratsa ta cikinsu...

RANA (THE SUN)

Image
  SCIENCE IN HAUSA: GRAND EPISODE 14 KARSHEN BABI NA FARKO RANA (THE SUN) Yau da gobe mukan wayi gari da haske wanda muke samu daga halitta mafi girma a cikin taurari. Wannan babbar halitta tanada sunaye dayawa amma a Hausance muna kiranta da Rana. Wannan kashin na SCIENCE IN HAUSA gagarumi ne domin shine zai rufe Babin Farko na ayyukana. Rana ta samu ne kimanin shekaru biliyan 4.5 daga tarwatsewar gajimare mai dauke da burbushin Hydrogen. Masana kimiyya sunawa wannan al'amari lakabi da "Big Bang Theory" wanda akansa ne mafi yawan ilmin kimiyya na taurari ya ta'allaka. Rana tana daukene da shimfidu har guda shida wadanda suka hada da; 1- Corona: Itace shimfidar farko wacce take fitarda hasken rana izuwa sauran Duniyoyin da suke zagaye da Ranar. 2- Mafitar Kyalli (Chromosphere): Wannan shimfida itace take canza siffar mahaski (photon) izuwa haske kafin yakai ga Corona. 3- Mafitar Wuta (Photosphere): Kafin mahaski yakai ga fita waje yana sauya launi ne daga burbushin He...

KWAYAR HALITTA (THE CELL)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 13 Kowacce halitta walau mutum, dabba ko tsirrai suna tattare ne da wasu kananun ginshikai wadanda sune tushen gabobi da kuma tsokar jikinsu. Wadannan abubuwa sune kwayar halittu (Turanci: Cell or Cells) wadanda sune ginshikan kowacce siffar kowacce halitta. Sunada kankatar da ido baya iya ganinsu face da na'urar hangen nesa (microscope). Kwayar halitta/halittu (daga yanzu KH) sune mafi kankantar siffa a jikin kowacce rai. A jikin mutum kadai akan samu KH kimanin trillion 50; a jikin yatsa ana iya samun kimanin miliyan 10. Yayinda a jikin silin gashi guda ana iya jera KH guda 10 saboda kankantarsu. Misalin KH da akan iya gani da ido itace kwaiduwa (egg yolk) wanda KH ce guda mai zaman kanta. Amfanin KH sun hada da samar da kuzari da kuma sinadaran gina jiki. KH ta kashi izuwa kashi biyu;  1- Eukaryotic: Wadannan ana samunsu ne a jikunan mutane da tsirrai. KH din eukaryotic suna tattare da kayan ciki (Organelles) wadanda suke kunshe da wadansu abubuwa...

KWAYAR ZARRA (THE ATOM)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 12 Dauki dutse guda kayi ta farfasashi; nasan zai kai matakin da bazaka iya fasashi ba saboda ya zama gari. Da zaka iya tattaro wannan garin ka hadeshi zaka samu dutsen ya dawo siffarsa. Wannan garin dauke yake da wasu kananun bangorai da ido baya iya gani; ana kiransu da kwayar zarra. Kwayar Zarra ((daga yanzu KZ) Turanci; Atom) itace mafi kankantar kowanne burbushi (element). Wadannan burbushi sune ginshikan kowacce siffa dake kewaye damu kamar duwatsu, iska, ruwa da makamantansu. Cikin kowanne burbushi akwai KZ wacce take kebanta da wasu halayya mabambantan juna. Tattare da kowacce KZ akwai wasu kananun ginshikai da sune suke dauke da halayyar burbushin KZ din; ana masu lakabi da sub-atomic particles a Turance. Wadannan ginshikan sun hada da protons, neutrons da electrons. -Proton: Wannan shine yake dauke da cajin dama (+) kuma da shine ake danganta mazaunin kowanne burbushi a Jadawalin Burbushi (Periodic Table of Elements). Adadin yawan protons na kow...

DAMARAR ASTEROID (THE ASTEROID BELT)

Image
 SCIENCE IN HAUSA: EPISODE 11 Sararin samaniya cike take da abubuwa da suke sanyawa ma'abota kwakkwafi zumudin ganewa idanunsu al'ajabin da yake tattare dasu. Damarar Asteroid (Turanci; Asteroid Belt) tana daya daga cikin tarin abubuwan mamakin dake kewaye da Duniyarmu. Wannan kashin na SCIENCE IN HAUSA zaiyi dubane ga bayanan da suke tattare da Damarar Asteroid. Damarar Asteroid wani yankine a sararin samaniya mai tattare da tarin duwatsu da bangorai da yake tsakanin duniyoyin Mars da kuma Jupiter; ana yiwa yankin da yake lakani da "Inner and Outer Planets Zone". Giuseppe Piazzi na kasar Italia shine wanda ake jinginawa gano Damarar Asteroid a cikin karni na Goma Sha Tara a shekarar 1801. Damarar Asteroid tana gewaya Rana ne kamar sauran duniyoyi sannan kuma yanada nisan a kalla kilomita tsakanin miliyan 327 zuwa 498 daga Ranar. A baya, masana kimiyya suna daukar duwatsu da kuma bangoran dake yankin Damarar Asteroid a matsayin wani yanki na wata Duniya data wanzu kaf...